Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Amurka ta sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da za su iya fuskantar takunkumin da ya shafi wasu nau’o’in tallafin soji, sayar da kayan aikin soja da shirye-shiryen haɗin gwiwar tsaro, sakamakon rahoton da ya yi zargin cewa ana ci gaba da ɗaukar yara da amfani da su a rikice-rikicen da suka shafi ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a ƙasar.
Rahoton jaridar Premium Times na ranar 13 ga Oktoba, 2026, ya bayyana cewa an saka Nijeriya cikin jerin ƙasashe 14 da rahoton Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka kan Fataucin Mutane na shekarar 2026 ya ambata ƙarƙashin dokar hana amfani da yara a yaƙe-yaƙe, wato Child Soldiers Preɓention Act (CSPA).
Rahoton ya zargi ƙungiyoyin Boko Haram da ISIS reshen Yammacin Afirka, wanda aka fi sani da ISWAP, da ci gaba da ɗaukar yara, sace su ko tilasta musu shiga ayyukan da suka shafi rikice-rikice da tashin hankali a Nijeriya.
A cewar rahoton, yaran na fuskantar amfani da su a ayyuka daban-daban, ciki har da leƙen asiri, ɗaukar saƙonni, tsaro da sauran ayyukan tallafa wa ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai. Wasu kuma ana amfani da su wajen kai hare-haren ƙunar baƙin wake.
Rahoton ya bayyana cewa wasu daga cikin yaran ana sace su ne ko kuma tilasta musu shiga ƙungiyoyin, yayin da wasu ke fuskantar cin zarafi da sauran matsaloli.
ƙarƙashin dokar CSPA, sanya wata ƙasa cikin wannan jerin na iya janyo mata takunkumin da ya shafi tallafin horar da jami’an soji, tallafin kuɗaɗen soji daga ƙasashen waje, bayar da kayan aikin soja da wasu lasisin sayar da kayan aikin soja kai tsaye.
Sai dai dokar ta tanadi wasu keɓancewa da kuma yiwuwar Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayar da rangwame daga takunkumin idan ya ga hakan ya dace, bisa tanadin dokar.
Rahoton ya ƙunshi ƙasashe 14, ciki har da Nijeriya, Afghanistan, Myanmar, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Habasha, Iran, Rasha, Rwanda, Somaliya, Sudan ta Kudu, Sudan, ɓenezuela da Yemen.
Rahoton ya shafi lokacin daga ranar 1 ga Afrilu, 2025, zuwa ranar 31 ga Maris, 2026, kuma ya nuna cewa takunkumin na iya shafar wasu fannoni na haɗin gwiwar tsaron Amurka da Nijeriya, musamman horar da jami’an tsaro da sayen kayan aikin soja.
Rahotannin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka na baya sun kuma yi magana kan yadda Boko Haram da ISWAP ke amfani da yara wajen ayyuka daban-daban, ciki har da ɗaukar saƙonni, tsaro, leƙen asiri da kai hare-hare.
Batun ya sake jawo hankali kan matsalar kare haƙƙin yara a yankunan da ke fama da rikice-rikicen tsaro, musamman Arewa maso Gabashin Nijeriya, inda ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya suka shafe shekaru suna kai hare-hare da sace mutane.
Sai dai sanya Nijeriya cikin jerin ba ya tabbatar da cewa sojojin ƙasar ko jami’an tsaronta ne ke ɗaukar yara aikin yaƙi. Rahoton ya danganta zargin amfani da yara a rikice-rikicen da ayyukan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP.
Matakin na ƙara matsin lamba kan gwamnatin Nijeriya wajen ƙarfafa matakan kare yara daga ɗaukar su ko amfani da su a rikice-rikice, tare da tabbatar da bin ƙa’idojin ƙasa da ƙasa da suka shafi kare yara a lokacin yaƙe-yaƙe.
