Rangwamen farashin man fetur ba yana nufin komawa ga tallafi ba ne — Idris

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na ƙasa, Mohammed Idris, ya bayyana cewa shirin Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPC Ltd.) na bayar da rangwamen farashin fetur na tsawon kwanaki 30 ba yana nufin komawa tsarin tallafin man fetur ba ne. Ya ce an tsara matakin ne domin rage wa ’yan Nijeriya raɗaɗin tashin farashin makamashi a kasuwannin duniya.

Idris ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja, yayin wani taron tattaunawa da manyan editoci da masu gabatar da shirye-shiryen kafafen watsa labarai, inda ya kare manufofin gyaran tattalin arziƙin gwamnatin tarayya tare da bayyana matakan da take ɗauka domin rage wa jama’a nauyin tsadar rayuwa.

Ministan ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta himmatu wajen inganta rayuwar jama’a, farfaɗo da tattalin arziƙi da kuma tabbatar da cewa alfanun gyare-gyaren da ake yi sun isa ga iyalai a faɗin ƙasar.

Da yake bayyana dalilin ƙaddamar da shirin NNPC, Idris ya ce kamfanin ya amince ya sadaukar da wani ɓangare na ribar da yake samu domin rage tasirin tsadar fetur ga masu saye.

“NNPC ta duba lamarin, ta ce: ‘To, muna samun wannan adadin riba. Me zai hana mu sadaukar da wani ɓangare na ribar da muke samu domin ’yan Nijeriya su samu ɗan sauƙi?’” in ji shi.

Ministan ya amince cewa iyalai na fuskantar matsin tattalin arziƙi, yana mai jaddada cewa dole ne manufofin gyaran tattalin arziƙin gwamnati su haifar da sauye-sauyen da jama’a za su iya gani a rayuwarsu ta yau da kullum.

Ya bayyana raguwar hauhawar farashin kayayyaki, ƙarfafa ajiyar kuɗaɗen waje da kuma ƙarin kuɗaɗen da ƙasar ke samu daga fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba a matsayin wasu alamomin samun ci gaba a tattalin arziƙi. Sai dai ya amince cewa akwai buƙatar tabbatar da cewa jama’a da dama sun fara jin amfanin wannan ci gaba.

“Aikin da ke gabanmu yanzu shi ne tabbatar da cewa ana jin tasirin wannan farfaɗowar tattalin arziƙi a fili a rayuwar ’yan Nijeriya da gidajensu,” in ji Idris.

Dangane da alaƙar gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago da kuma hauhawar tsadar rayuwa, ministan ya nuna kyakkyawan fata cewa gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin ƙwadago za su warware matsalolin da suka rage ta hanyar tattaunawa.

Ya kuma tuna da matsayar Shugaba Tinubu cewa za a iya duba tsarin mafi ƙarancin albashi duk bayan shekaru uku maimakon shekaru biyar.

Game da ’yancin kuɗi na ƙananan hukumomi, Idris ya sake jaddada aniyar gwamnatin wajen tabbatar da aiwatar da wannan tsarin. Ya bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin warware matsalolin aiwatarwa da kuma tabbatar da cewa tsarin yana aiki yadda ya kamata.

A ɓangaren samar da wadataccen abinci, ministan ya bayyana ƙoƙarin gwamnati na ƙara yawan amfanin gona a cikin gida da kuma ƙarfafa ajiyar abinci na musamman domin inganta samuwa da sauƙin farashin kayan abinci.

Ya kuma yi kira ga ’yan kasuwa da su guji ɓoye kayan abinci ko shiga harkokin da za su haifar da ƙarancin kayayyaki na bogi a kasuwa. Ya ce haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu na da muhimmanci wajen rage wa masu saye nauyin tsadar rayuwa.

“Gwamnati za ta iya samar da hanyoyin da za su ba ’yan Nijeriya sauƙi, amma a ƙarshe, ya rataya a wuyan ’yan Nijeriya su ma su goyi bayan abin da gwamnati ke yi,” in ji shi.

Idris ya kuma kare ayyukan hanyoyin mota da gwamnatin tarayya ke gudanarwa, yana mai cewa an tsara su ne domin inganta zirga-zirga, sauƙaƙa kasuwanci, tallafa wa noma da kuma samar da manyan hanyoyin tattalin arziƙi da za su taimaka wa harkokin kasuwanci su bunƙasa.

Ya yi watsi da ra’ayin cewa ana gudanar da ayyukan ne saboda la’akari da zaɓe, yana mai cewa gina ababen more rayuwa ya zama dole domin haɗa birane da faɗaɗa damar tattalin arziƙi.

“Ba wanda yake gyaran hanya kawai saboda zaɓe ya zo. Muna gyaran hanyoyi ne domin ’yan Nijeriya su samu damar yin amfani da su, su haɗa birane tare da samar da manyan hanyoyin tattalin arziƙi da za su ba harkokin kasuwanci damar bunƙasa,” in ji shi.

Dangane da tsaro, ministan ya bayyana cewa an faɗaɗa tsarin rundunonin sojoji daga runduna takwas zuwa 12, tare da inganta tallafin da ake bai wa jami’an tsaro.

Duk da cewa ya amince akwai manyan ƙalubalen tsaro da har yanzu ake fuskanta, ya sake jaddada aniyar gwamnati ta ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Da yake amsa tambayoyi kan ’yancin aikin jarida da rahotannin kama wasu ’yan ƙasa sakamakon bayyana ra’ayoyinsu na siyasa, Idris ya ce bai san da wata umarni daga Shugaba Tinubu da ta ba da izinin danniya ko tauye ’yancin kafafen yaɗa labarai ba.

Sai dai ya yi alƙawarin neman ƙarin bayani kan takamaiman abubuwan da aka gabatar masa yayin taron.

Ministan ya kuma yi kira ga ƙungiyoyin yaɗa labarai da su kiyaye ƙa’idojin aikin jarida, su tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafawa, tare da guje wa kanun labarai masu yaudarar jama’a ko tayar da hankali. Ya jaddada cewa ’yancin aikin jarida dole ne ya kasance tare da ɗaukar nauyin da ke tattare da shi.

“’Yancin aikin jarida ba wani abu ba ne da yake rataye a sararin sama kawai. Akwai wani abu da ya kamata ya kasance tare da shi, wato alhakin waɗanda suke amfani da wannan ’yanci,” in ji shi.

Idris ya yaba wa kafafen yaɗa labaran da suka halarci taron saboda yadda suka shiga tattaunawar, tare da bayyana shirinsa na ci gaba da gudanar da irin waɗannan zaman, mai yiwuwa duk bayan mako biyu.

Ya ce tattaunawar kai tsaye a kai a kai za ta ƙarfafa sadarwa tsakanin gwamnatin tarayya da kafafen yaɗa labarai, ta samar da damar fayyace manufofin gwamnati, tare da ba da damar amsa matsalolin ƙasa da suka taso cikin gaggawa.

By ukarofi

Leave a Reply