Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta soke dokar tabar wiwi, ta kuma sauya fasalin dokokin NAFDAC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa da ta soke Dokar Tabar Wiwi ta Nijeriya da kuma dokar da ake amfani da ita wajen tafiyar da Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi (NDLEA), a wani yunƙuri na sake fasalin dokokin ƙasar da suka shafi yaƙi da miyagun ƙwayoyi.

Haka kuma, an gabatar da wani kudirin doka dabam da ke neman ƙarfafa ikon Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC), domin ta fi dacewa da sababbin ƙalubalen da suka shafi lafiyar jama’a da kuma sauye-sauyen ƙa’idojin kula da kayayyakin lafiya a duniya.

A cikin wasiƙar da ya aika wa Majalisar Dattawa, wadda Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta yayin zaman majalisar na ranar Talata, Tinubu ya ce kudirin dokar NDLEA na shekarar 2026 na neman soke dokar NDLEA mai lamba Cap. N30 da kuma Dokar Tabar Wiwi mai lamba Cap. I6, waɗanda ke cikin kundin dokokin Tarayyar Nijeriya na shekarar 2004.

ƙudirin ya kuma tanadi samar da cikakken tsarin doka guda ɗaya da zai jagoranci aiwatar da dokokin da suka shafi yaƙi da noma, sarrafawa, safara, fatauci da amfani da miyagun ƙwayoyi ba bisa ƙa’ida ba. Haka kuma, zai bai wa hukumar ƙarin iko wajen gudanar da bincike kan mutanen da ake zargi da hannu a ayyukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi.

An aika da kudirin ne bisa tanadin sashe na 58(2) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na shekarar 1999, kamar yadda aka yi masa gyara. Daga nan, an miƙa shi ga Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Dokokin Zama da Harkokin Kasuwanci domin ɗaukar matakan da suka dace.

A wani ɓangare na zaman majalisar, Sanata Suleiman Sadiƙ ya gabatar da kudirin dokar sake kafa dokar NAFDAC, yana mai cewa dokar da ake amfani da ita a yanzu ba ta wadatar wajen tunkarar sababbin ƙalubalen da suka shafi lafiyar jama’a, duk da gudummawar da hukumar ke bayarwa wajen kula da abinci, magunguna da sauran kayayyaki.

Ya bayyana cewa dokar ta kasance muhimmin ginshiƙi wajen kafa NAFDAC a matsayin ɗaya daga cikin manyan hukumomin Nijeriya masu kula da lafiyar jama’a, inda ta taka rawar gani wajen daidaita harkokin abinci, magunguna, kayan kwalliya, na’urorin lafiya, sinadarai, ruwan sha da aka sarrafa da sauran kayayyakin da suka shafi lafiya.

Sai dai Sanata Sadiƙ ya ce ci gaban kimiyya da fasaha, tare da ƙara ƙwarewar masu safarar jabun kayayyaki ta kan iyakoki, sun bayyana wasu gibi a cikin dokar da ake amfani da ita a halin yanzu.

Ya ce: “Yanayin ƙa’idojin kula da kayayyaki a duniya ya sauya matuƙa. Sabbin binciken kimiyya sun samar da wasu nau’o’in kayayyaki da ke buƙatar kulawa ta musamman, yayin da safarar jabun kayayyaki ta ƙetare iyakoki ta ƙara zama mai sarkakiya.”

Ya lissafa fasahar kimiyyar halittu, basirar kwamfuta ta wucin gadi (AI), na’urorin zamani na kula da lafiya, hanyoyin gano cututtuka, kayayyakin halittu da sinadaran da ake amfani da su wajen ƙera magunguna a matsayin wasu sabbin abubuwa da suka zama muhimman ɓangarorin harkokin kiwon lafiya na zamani, amma dokar da ake amfani da ita ba ta fayyace yadda za a kula da su yadda ya kamata ba.

A cewarsa, wannan yanayi ya sa ya zama wajibi a soke dokar gaba ɗaya tare da sake kafa sabuwar doka mai hangen nesa, wadda za ta iya tunkarar ƙalubalen da ake fuskanta a yanzu da kuma waɗanda za su iya tasowa nan gaba.

Sanatan ya bayyana cewa sabuwar dokar da ake shirin kafa wa za ta ƙarfafa ikon NAFDAC wajen gudanar da bincike da aiwatar da dokoki. Za ta bai wa jami’an da aka amince da su damar binciken wurare da ababen hawa, ƙwace ko tsare kayayyakin da ba su dace da doka ba, rufe wuraren da ake aikata laifuka da kuma neman umarnin kotuna masu hurumin shari’a.

Ya ƙara da cewa kudirin zai sauya tsarin gudanarwar hukumar, ya sabunta tsarin mambobin majalisar gudanarwarta, ya ƙarfafa hanyoyin tabbatar da gaskiya da riƙon amana, tare da zamanantar da tsarin kuɗaɗenta da yadda take tafiyar da harkokin kuɗi.

A cewarsa, sauye-sauyen za su inganta ingancin ayyukan hukumar tare da tabbatar da cewa duk matakan tilasta bin doka suna gudana bisa ƙa’idojin shari’a da tanade-tanaden kundin tsarin mulki.

Sadiƙ ya ce sake kafa dokar gaba ɗaya zai kuma taimaka wajen fayyace tanade-tanadenta, kawar da saɓani tsakanin wasu dokoki da samar da tsari guda ɗaya mai sauƙin fahimta ga hukumomin sa ido, masana’antun ƙera kayayyaki, ƙwararrun ma’aikatan lafiya, masu zuba jari da kotuna.

Ya ce: “A ƙarshe, wannan kudirin doka ya shafi kare rayuka da lafiyar ’yan Nijeriya, ƙarfafa amincewar jama’a ga tsarin kiwon lafiyarmu, bunƙasa masana’antun cikin gida, sauƙaƙa kasuwanci na halal, inganta ayyukan hukumomin sa ido da kuma tabbatar da cewa tsarin kula da abinci da magunguna na Nijeriya yana dacewa da sauye-sauyen duniya da ƙalubalen da ke tasowa.”

Baya ga waɗannan kudirori, an kuma miƙa wa Majalisar Dattawa kudirin gyara Dokar Hukumar Binciken Haɗurra ta Nijeriya (NSIB) na shekarar 2026.

ƙudirin na neman faɗaɗa ayyukan hukumar daga binciken haɗurran jiragen sama kaɗai zuwa haɗurran da suka shafi sufurin ruwa da sauran hanyoyin sufuri.

Haka kuma, yana neman mayar da hukumar ƙarƙashin kulawar Fadar Shugaban ƙasa tare da ƙarfafa tsarin gudanarwarta, ayyukanta da ikon da take da shi na gudanar da harkokinta.

An miƙa wannan kudiri ma ga Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Dokokin Zama da Harkokin Kasuwanci domin ci gaba da aikin majalisa a kansa.

By ukarofi

Leave a Reply