‘Yan kasuwa sun ƙi amince wa buƙatar Gwamnatin Tarayya ta tsayar da farashin fetur a N1,350

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

‘Yan kasuwar fetur sun yi watsi da buƙatar Gwamnatin Tarayya ta neman a tsayar da farashin litar fetur zuwa N1,350, inda suka tirje akan kasuwanni, gasa da ingancin rabawa sune za su yanke farashin a fannin samar da fetur na Nijeriya.

Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Muhimman Makamashi ta Ƙasa (MEMAN), ta ce iyakance farashi daga ɓangaren gwamnati ba shi zai warware matsalolin ƙalubalen da ake fuskanta ba a kasuwar fetur, inda ta yi kira da a samar da matakan daidaita farashi domin magance matsalolin rabawa da rage adadin kuɗaɗen gudanarwa.

Wannan mataki na zuwa ne ƙasa da makonni uku da Ministan Tattali, Taiwo Oyedele ya sanar da cewa Gwamnatin Tarayya tana tattaunawa da ‘yan kasuwa domin kada farashin ya wuce N1,350, wanda a ƙarƙashinsa, masu tacewa da shigowa da shi za su haƙura da tsadarsa da dawo da abin da suka rasa daga bisani idan halin kasuwa ya inganta.

Ya bayyana cewa, wannan buƙata idan aka amince da ita, za a riƙa yin nazari akanta a kowane wata, wadda an shirya ta ne da nufin daidaita kwan-gaba kwan-bayan farashin a madadin dawo da tallafin fetur da aka cire a watan Mayun 2023.

MEMAN a nata ɓangaren, ta yi kira sa a samar da tsarin rabawa mai faɗin ta yadda zai bayar da damar samuwarsa a wadace da daidaita farashi, wanda zai kuma taimaka wa daidaita farashi da sauke wasu nauye-nauyen kwangila.

A cewarta, samar da tsarin gudanarwa mai kyau shi ne zai bayar da damar gasa, inganta tsaron rabawa da tallafa wa kyawawan sakamako ga kwastomomi ba tare da dogaro da kulawar farashi daga ɓangaren gwamnati ba.

By Babaji

Leave a Reply