Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Tashin hankali ya sake ɓarkewa a kan hanyar Magami zuwa Dansadau a Jihar Zamfara yau Juma’a, yayin da yan bindiga suka sake tare hanyar tare da lalata motoci da dukiyoyin al’umma.
Lamarin ya faru ne bayan sanarwar da yan bindigan suka yi a baya cewa za su ƙone motoci har guda 250 a kan hanyar.
Rahotanni daga yankin na cewa ‘yan bindigan sun aiwatar da barazanar tasu, inda suka tare hanyar tare da ƙone motoci da dama tare da wawashe dukiyoyin fasinjoji.
Wannan mummunan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar Dansadau da kewayenta ke fuskantar ƙarancin kayan masarufi da magunguna sakamakon tare hanyar da aka yi a baya.
Mazauna yankin na cikin fargaba da tsoro, yayin da zirga-zirgar ababen hawa ta tsaya cak sakamakon hare-haren.
Al’ummar yankin sunyi kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara da Gwamnatin Tarayya da su gaggauta ɗaukar matakin tsaro don ceto rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sun kuma yi kira ga gwamnatin Jihar da ta buɗe hanyar Magami-Dansadau domin kai ɗaukin agaji ga al’ummar da abin ya shafa.
