DSS ta cafke ɗan tsohon shugaban hukumar fansho, Faisal Maina bayan shekara shida ana neman sa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta ce ta yi nasarar kama Faisal, wato ɗan Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban rusashshiyar hukumar gyaran fansho (PRTT).

Majiyoyi sun shaida wa manema labarai cewa, an damƙa Faisal ga Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) bayan cika hannu da shi.

An yi nasarar kamen ne sakamakon amfani da wasu bayanan sirri da ke nuna cewa Faisal ya dawo Nijeriya a sirrance tun bayan da jami’an tsaro suka fara farautar sa a shekarar 2020.

Majiyar da ta bayyana haka, ta kuma ce EFCC ta gurfanar da shi bisa tuhume-tuhume guda uku masu alaƙa da sauya akalar wasu kuɗaɗe. Jami’an DSS sun gano tare da kama Faisal ne a yakin Karsana da ke Abuja kafin suka miƙa shi ga EFCC.

By Babaji

Leave a Reply