Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Laifukan Tattalin Arziki ta Nijeriya (EFCC) ta gargaɗi ’yan mata da su guji faɗawa tarkon cin zarafin jima’i ta intanet, wanda ake amfani da hotuna ko bayanan sirri wajen yi wa mutum barazana da karɓar kuɗi, tare da nisantar shiga harkokin laifukan yanar gizo.
Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ne ya yi wannan gargaɗi a ranar Litinin, 12 ga Oktoba, 2026, a Abuja, yayin wani taro da ƙungiyar African Girl Guild ta shirya domin bikin Ranar ’Ya Mace ta Duniya. Taken taron shi ne: “Zuba Jari a Cikinta, ƙarfafa Mata da Ba Su Damar Jagoranci.”
Olukoyede, wanda Shugabar Sashen Wayar da Kai da Sauya Tunani na EFCC, Mataimakiyar Kwamandan Hukumar, Aisha Muhammed, ta wakilta, ya ce masu aikata laifukan suna amfani da raunin da wasu ’yan mata ke nunawa a cikin alaƙar soyayya wajen yi musu barazana da karɓar kuɗi.
Ya shawarci ’yan matan da su yi taka-tsantsan wajen shiga alaƙa da mutane, tare da guje wa duk wani abu da zai ba masu aikata laifuka damar cin zarafinsu.
“Ya kamata ’yan mata su yi hankali a cikin alaƙarsu da mutane, kada su faɗa tarkon masu aikata laifuka da masu amfani da barazanar fallasa hotunan sirri domin karɓar kuɗi. Mutunci a cikin alaƙa zai kare ki daga irin waɗannan mutane. Mace mai mutunci za ta fi mace mai kwalliya kawai daraja a ƙarshe. Mutuncinki shi ne kambunki; kada ki sayar da shi a kan farashi mai sauƙi,” inji shi.
Shugaban EFCC ya kuma gargaɗi ’yan matan kan shiga laifukan yanar gizo, ciki har da bayar da asusun bankinsu domin masu damfara su riƙa karɓa ko tura kuɗaɗen haram ta cikinsu, da kuma yi wa mutane barazana ko baƙar magana ta intanet domin karɓar kuɗi.
Ya ce shiga irin waɗannan ayyuka ba kawai laifi ba ne, har ma yana ɓata sunan Nijeriya, ƙasar da matasan za su buƙaci ta wajen neman ilimi, aiki da sauran damammaki a nan gaba.
Olukoyede ya yi kira ga ’yan matan da su zama ’yan ƙasa nagari ta hanyar kai rahoton abubuwan da ba su dace ba, bayar da gudummawa ga al’umma da kuma bin doka.
Ya ce mace mai kishin ƙasa tana bayar da rahoton laifi, tana sa kai wajen ayyukan alheri, tana mutunta doka, kuma tana fahimtar cewa ita ma tana da rawar takawa wajen gina Nijeriya.
Shugaban hukumar ya kuma ƙarfafa ’yan matan da su koyi sana’o’i da dabarun da za su taimaka musu wajen samun kuɗi ta halal, yana mai lissafa fasahar zamani, ɗinki, yin kek da sauran kayan zaƙi, ƙirƙirar abubuwan da ake wallafawa a intanet da kuma koyon rubuta manhajojin kwamfuta a matsayin wasu daga cikin sana’o’in da za su iya koya.
Ya shawarce su da su riƙa tanadin wani kaso na kuɗaɗen da suke samu, maimakon kashe su gaba ɗaya, tare da koyon bambance buƙatun yau da kullum da abubuwan da za su iya jira.
“Ku koyi yadda ake samun kuɗi ta halal. Ku koyi sana’a, kamar fasahar zamani, ɗinki, yin kek, ƙirƙirar abubuwan da ake wallafawa a intanet ko rubuta manhajojin kwamfuta. Ba duk kuɗin da kuka samu za ku kashe ba; ku riƙa ajiye wani kaso, misali kashi 20 cikin 100, sannan ku san bambanci tsakanin buƙatunku da abubuwan da kuke so kawai.
“Sanin yadda ake tafiyar da kuɗi kariya ce ga mutum. Kada ku bari wani ya yi amfani da asusunku wajen aikata zamba, domin asusun da ke ɗauke da sunanku zai iya kai ku gidan yari,” inji shi.
Olukoyede ya ce samun ’yancin kai ta fuskar kuɗi zai taimaka wa ’yan mata wajen tsayawa da ƙafafunsu, kare kansu daga cin zarafi da kuma yanke shawarar da ta dace game da makomarsu.
Ya bayyana cewa yarinya mai ƙwarewa da ilimi, wadda take samun kuɗinta ta halal, za ta fi samun damar kare kanta daga masu son amfani da ita, domin ba za a iya sayen lamirinta cikin sauƙi ba.
Shugaban EFCC ya ƙara da cewa hukumar ta kafa ƙungiyoyin Integrity Clubs da Zero Tolerance Clubs a makarantu daban-daban a faɗin Nijeriya domin inganta ɗabi’ar gaskiya da mutunta doka a tsakanin matasa.
Ya yi kira ga ɗaliban da su zama jakadun gaskiya da riƙon amana a makarantu da al’ummominsu.
A wajen taron, Denen Petronella, mataimakiya ta musamman ga Jindu Peter, wanda ya kafa ƙungiyar African Girl Guide, ta ce bai wa ’yan mata muhimmanci ya haɗa da samar musu da ilimi, kariya, jagoranci, horo da damammakin da za su taimaka musu wajen gano ƙwarewarsu da cimma burinsu.
Ta bayyana cewa bai kamata a tsaya kawai wajen ƙarfafa ’yan mata da kalaman cewa za su iya yin nasara ba; ya kamata a samar musu da tsarin tallafi da damar da za su taimaka musu wajen cimma burinsu.
A matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙungiyar na ƙarfafa ’yan mata, an sanar da ƙaddamar da Camp Amani School Club na African Girl Guide. An bayyana cewa ƙungiyar za ta samar wa ɗalibai da dama ta koyon jagoranci da dabarun rayuwa, ƙara musu ƙarfin gwiwa da kuma gano sabbin damammaki a tsawon shekarar karatu.
Taron ya samu halartar wakilan ma’aikatun gwamnati, hukumomi da cibiyoyi daban-daban, tare da ɗalibai daga makarantun sakandare a Abuja.
