Dan ƙabilar Idoma ba zai taɓa zama gwamnan Benuwe ba – Lawani

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Benuwe, Cif Steɓen Lawani, ya ce ya yi ƙoƙarin zama gwamnan jihar, amma ya fahimci cewa siyasar ƙabilanci ta zama babban cikas ga burin ɗan ƙabilar Idoma na jagorantar jihar.

Lawani, wanda ya taɓa zama mataimakin gwamna a ƙarƙashin tsohon Gwamna Gabriel Suswam daga shekarar 2007 zuwa 2011, ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Daily Trust, inda ya yi tsokaci kan rayuwarsa, tafiyarsa a siyasa, harkokin kasuwancinsa da matsalolin tsaro da tattalin arzikin Nijeriya. Ya ce bai yi nasarar zama gwamna ba ba wai don an ɗauke shi a matsayin mutumin da ba shi da ƙwarewa ba, sai dai saboda manyan ƙabilun jihar ba su shirya miƙa mulki ga ƙaramar ƙabila ba.

“Na yi ƙoƙari, amma a ƙarshe na ce na gaji. Ba zan ƙara wahalar da kaina ba, domin na fahimci cewa babu damar ɗan Idoma ya zama gwamnan Jihar Benuwe,” inji shi.

Sai dai ya ce har yanzu yana fatan wata rana wannan tunani zai sauya, yana mai cewa ya yi ƙoƙarin tsayawa takara domin kada al’ummar Idoma su zarge shi da rashin yunƙurin neman shugabancin jihar.

Lawani ya bayyana cewa a shekarar 2023 ya sake neman tikitin takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC, amma ya janye daga takarar ne a ranar da za a gudanar da zaɓen fidda gwani, bayan shugabannin jam’iyyar sun sauya tsarin zaɓen daga na wakilai zuwa na kai tsaye.

Ya ce shi da wasu manyan ’yan siyasa a jihar, ciki har da Sanata Barnabas Gemade da tsohon Antoni Janar na Tarayya, Michael Aondoakaa, sun yi imanin cewa za su yi nasara a zaɓen fidda gwani da aka tsara tun farko.

Sai dai, a cewarsa, sauya tsarin a ranar zaɓen ya nuna cewa an riga an yanke shawarar wanda ake son ya yi nasara. “Dukkanmu mun amince cewa za a yi zaɓen fidda gwani ta hanyar wakilai, kuma a kan wannan tsarin muka gudanar da yaƙin neman zaɓenmu. Amma ranar zaɓe aka sauya ƙa’ida, aka ce za a yi zaɓen kai tsaye. Na janye daga takarar lokacin da aka bayar da wannan umarni,” inji shi.

Lawani ya bayyana cewa a lokacin da ya nemi takarar gwamna bayan kammala wa’adinsa na mataimakin gwamna, tsohon Gwamna Suswam bai mara masa baya ba, amma ya ce matsalar ta fi alaƙa da yadda wasu manyan ƙabilun Benuwe suka nuna rashin shirin miƙa mulki ga ƙaramar ƙabila.

Ya ce ya sha kayar da mutumin da daga baya ya zama gwamna a zaɓen fidda gwani, amma abokin hamayyarsa ya koma wata jam’iyya inda ya samu nasara a babban zaɓe.

A cewarsa, wannan lamari ya ƙara tabbatar masa da irin tasirin ƙabilanci a siyasar Benuwe, wanda ya ce har yanzu bai gushe ba.

Lawani ya kuma bayyana cewa, duk da rashin samun tikitin gwamna, bai daina shiga harkokin siyasa ba. Ya ce Sanata George Akume, tsohon gwamnan Benuwe kuma jagoran APC a jihar, ya nemi taimakonsa wajen yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Tinubu, kuma ya amince ya yi aiki don ganin jam’iyyar ta samu nasara.

Ya ce a lokacin da aka nemi taimakonsa, yana Dubai, amma ya dawo Nijeriya domin gudanar da aikin siyasa a Benuwe na tsawon wasu watanni.

Sai dai ya ce duk da gudunmawar da ya bayar, bai samu muƙamin minista da aka taɓa sanar da shi cewa za a ba shi ba. “An gaya mini cewa za a naɗa ni minista, kuma na yi godiya ga waɗanda suka yi wannan shiri. Amma kwanaki uku ko huɗu kafin sanar da sunayen ministocin, aka sake kirana aka ce ba a saka sunana ba. Na ce babu damuwa. Ba na riƙe ƙiyayya ga kowa, domin ba shi ne karo na farko da irin wannan abu ya faru da ni ba,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, an kuma gaya masa cewa Shugaba Tinubu na da niyyar naɗa shi jakadan Nijeriya a wata muhimmiyar ƙasa, amma ya ƙi amincewa da tayin saboda yana da sana’o’insa kuma ba ya neman muƙami domin samun abin dogaro da kai.

Da yake magana kan shekarunsa takwas a matsayin mataimakin gwamnan Benue, Lawani ya ce yana da kyakkyawar alaƙa da tsohon Gwamna Gabriel Suswam, sabanin yadda aka saba samun saɓani tsakanin gwamnonin jihohi da mataimakansu. Ya ce sun yi aiki cikin fahimtar juna, kuma Suswam ya riƙa sanar da shi duk lokacin da zai bar jihar, ta yadda zai iya tsara nasa ayyukan ba tare da tangarda ba.

Lawani ya ce shi ne ke kula da harkokin ƙananan hukumomi a lokacin, duk da cewa ba kwamishina ne ba, kuma yana yawan tattaunawa da gwamnan kan yadda za a gudanar da ayyukan gwamnati. “Idan kana mataimakin wani, kuma ya amince da kai har ya ba ka ’yancin gudanar da ayyukanka, to wawa ne kawai zai yi amfani da wannan amana ta hanyar da ba ta dace ba. Idan kuma ba ka ci amanar da aka ba ka ba, za ka zauna lafiya,” inji shi.

Ya ce ya yi farin cikin yadda suka gudanar da shekaru takwas ɗin, domin ba su samu wata babbar matsala tsakaninsu ba.

Tsohon mataimakin gwamnan ya bayyana cewa matsalar tsaro da tsadar rayuwa na daga cikin manyan ƙalubalen da Nijeriya ke fuskanta, yana mai cewa ya kamata Gwamnatin Tarayya ta ɗauki lamarin a matsayin dokar ta-ɓaci ta ƙasa. Ya ce rashin tsaro ya hana manoma zuwa gonakinsu, wanda hakan ke ƙara jawo tashin farashin kayan abinci a kasuwanni.

By ukarofi

Leave a Reply