Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci mawallafan intanet su tabbatar da sahihancin labarai

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga mawallafan labarai na intanet da sauran ma’aikatan kafafen yaɗa labarai na zamani a Nijeriya da su tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafawa ko yaɗa su, musamman a wannan lokaci da kafafen sada zumunta suka sauƙaƙa wa kusan duk mai wayar salula damar samarwa da yaɗa labarai.

Ministan ya yi wannan kiran ne a wani taron kwana ɗaya da aka gudanar a Abuja, wanda ƙungiyar Masu Rubutun Intanet, Masu Wallafa Labarai a Intanet da Masu Samar da Abubuwan Yaɗa Labarai ta Jihar Neja (Niger Bloggers, Online Publishers and Content Deɓelopers Group) ta shirya, ƙarƙashin taken “Nijeriya Farko, Kafin Komai.”

Alhaji Mohammed Idris ne ya karɓi baƙuncin taron, wanda Yahaya Mohammed Usman da Nurudeen Isiyaku Daza suka jagoranta.

A jawabinsa, ministan ya jaddada muhimmancin kiyaye gaskiya, ƙwarewa da la’akari da muradun ƙasa wajen yanke shawarwarin edita. Ya bayyana cewa kafafen yaɗa labarai na gargajiya suna da tsare-tsaren tantance bayanai da ke taimakawa wajen tabbatar da sahihancin labaran da ake wallafawa.

Ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su goyi bayan sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa, yana mai jaddada cewa haɗin kai yana da muhimmanci wajen cimma burin ci gaban ƙasa.

Idris ya yi alƙawarin ci gaba da gudanar da tarurruka a kowace kwata ta shekara tare da mawallafan intanet, masu wallafa labarai da masu samar da abubuwan yaɗa labarai na Jihar Neja. Ya kuma bayyana aniyarsa ta mayar da tarurrukan na gaba zuwa na kwana biyu domin samar da ƙarin damar bunƙasa ƙwarewa, musayar ilimi da faɗaɗa yawan mahalarta.

Tun da farko, babban baƙon da ya gabatar da jawabin musamman a taron, Dakta Yunusa Umar, ƙwararre a harkokin ƙasashen waje da nazarin yankuna daga Jami’ar Nazarin Harsunan ƙasashen Waje ta Beijing da ke ƙasar China, ya buƙaci ’yan Nijeriya da su guji yaɗa labaran da za su ɓata sunan ƙasarsu saboda fushi ko takaici.

Umar ya jaddada muhimmancin kishin ƙasa da sadarwa mai nagarta, yana mai gargaɗin cewa yaɗa labaran ƙarya ko waɗanda ke nuna Nijeriya a mummunan yanayi na iya lalata martabar ƙasar a idon duniya.

Da yake ba da misali daga abin da ya faru da shi, Umar ya bayyana cewa an taɓa hana shi bizar shiga wata ƙasa, lamarin da ya danganta da yaɗuwar munanan labarai game da Nijeriya a kafafen sada zumunta a lokacin.

Ya kuma kwatanta ’yancin faɗin albarkacin baki da ake da shi a Nijeriya da takunkumin da ake fuskanta a wasu ƙasashe, ciki har da China. Ya ce ya kamata ’yan Nijeriya su yi amfani da wannan ’yanci cikin sanin ya kamata, tare da yin la’akari da illolin kalaman da suke furtawa ko wallafawa a bainar jama’a.

A saƙon fatan alheri da ya gabatar, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban ƙasa kan Kafafen Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Malam Abdulaziz Abdulaziz, ya buƙaci ma’aikatan kafafen yaɗa labarai da su kiyaye gaskiya, adalci, ƙwarewa da ɗa’ar aikin jarida.

Abdulaziz ya amince da haƙƙin ’yan ƙasa na sukar manufofin gwamnati da ayyukan jami’anta kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tanada. Sai dai ya jaddada cewa ya kamata irin wannan suka ta kasance mai ma’ana, mai tushe kuma mai kiyaye gaskiya, tare da la’akari da muradun ƙasa.

A ƙarshen taron, mawallafan intanet, masu wallafa labarai da masu samar da abubuwan yaɗa labarai daga Jihar Neja sun sha alwashin inganta aikin jarida mai nagarta, bayar da rahoto bisa gaskiya da kare muradun Nijeriya, tare da ci gaba da amfani da haƙƙinsu na kundin tsarin mulki wajen yi wa jami’an gwamnati tambayoyi da tuhumar ayyukansu.

Mahalartan sun kuma amince da wasu ƙudurori da suka ɗauki alƙawarin kiyaye manyan ƙa’idojin aikin jarida, ɗa’a da mu’amala mai kyau da jama’a.

Sun sake jaddada aniyarsu ta taimakawa wajen nuna Nijeriya a hanya mai kyau, tare da riƙe alhakin tantance ayyukan jami’an gwamnati ta hanyar rahotanni masu gaskiya da suka mai ma’ana.

A ƙarshe, mahalartan sun gode wa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, bisa karɓar baƙuncin taron da kuma alƙawarin ci gaba da tattaunawa da ma’aikatan kafafen yaɗa labarai na zamani daga Jihar Neja.

Sun kuma yaba wa Malam Abdulaziz Abdulaziz bisa gudunmawar da ya bayar a tattaunawar da ta shafi inganta aikin jarida da bunƙasa ƙasa.

ƙungiyar ta yi alƙawarin amfani da ilimin da aka samu a taron wajen ƙarfafa kishin ƙasa, bunƙasa ƙwarewar aikin jarida da tabbatar da amfani da kafafen yaɗa labarai na zamani cikin gaskiya, ƙwarewa da ɗa’a.

By ukarofi

Leave a Reply