Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kwamitin Majalisar Wakilai ta Nijeriya mai kula da asusun gwamnati ya gayyaci manyan jami’an Hukumar Kula da Basussukan ƙasa (DMO) da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Nijeriya (TCN) domin su yi bayani kan zarge-zargen karya ƙa’idojin rance da kuma gazawar karɓo basussukan gwamnati da suka kai ɗaruruwan biliyoyin naira.
An tsara zaman sauraron bayanan ne a ranar Litinin da Talata, biyo bayan wasu tambayoyi da aka gabatar a cikin rahoton Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Tarayya na shekarar 2024. Gayyatar na daga cikin ƙoƙarin kwamitin na tabbatar da bin ƙa’idojin kula da kuɗaɗen gwamnati da kuma ɗora wa ma’aikatu, hukumomi da sauran cibiyoyin gwamnatin tarayya alhakin yadda suke gudanar da harkokin kuɗaɗe.
Kwamitin, wanda ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Ede ta Arewa da Kudu, Ejigbo da Egbedore a Jihar Osun, Bamidele Salam, ke jagoranta, zai binciki zarge-zargen da suka shafi karɓar bashi ba bisa ƙa’idoji ba da kuma yadda ake ƙoƙarin karɓo basussukan da ake bin wasu hukumomin gwamnati. A cikin takardar gayyata mai ɗauke da ranar 29 ga Satumba, 2026, wadda manema labarai suka gani, kwamitin ya umarci hukumomin biyu da su miƙa dukkan takardun da aka buƙata zuwa sakatariyar kwamitin da ke ɗakin sauraron ƙorafe-ƙorafe na huɗu, a White House, cikin harabar Majalisar Wakilai, aƙalla sa’o’i 72 kafin ranar da aka tsara za su bayyana.
Haka kuma, takardar ta buƙaci manyan jami’an kula da asusun hukumomin da ƙwararrun da suka dace da batutuwan da za a tattauna su halarci zaman da ƙarfe 1 na rana a ɗakin sauraron ƙorafe-ƙorafe mai lamba 446. Ana sa ran Hukumar Kula da Basussukan ƙasa (DMO) za ta yi bayani kan zargin kasa bin adadin bashin da aka amince ta karɓa a cikin dokokin kasafin kuɗi guda biyar da suka shafi shekarun kuɗi daga 2020 zuwa 2024.
Rahoton shekara-shekara na Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Tarayya kan rashin bin ƙa’idoji da raunin tsarin kula da kuɗaɗe a ma’aikatu da hukumomin gwamnati, wanda ya ƙare a ranar 31 ga Disamba, 2024, ya nuna cewa hukumar ta zarce adadin bashin da aka amince mata ta karɓa da naira tiriliyan 54.57 a cikin waɗannan shekaru biyar.
Rahoton ya ce hukumar ta karɓi sababbin basussukan cikin gida da na ƙasashen waje da jimillarsu ta kai naira tiriliyan 88.67, sabanin naira tiriliyan 34.89 da aka tanada domin biyan buƙatun kuɗaɗen bashi a kasafin kuɗin gwamnatin tarayya da aka amince da shi a wannan lokaci.
Bambancin da ke tsakanin adadin bashin da rahoton ya bayyana da wanda aka ware a kasafin kuɗi ya haifar da tambayoyi kan ko hukumar ta bi ƙa’idojin da Majalisar Tarayya ta amince da su, da kuma hanyoyin da doka ta shimfiɗa na karɓar bashin gwamnati. Ana sa ran kwamitin zai nemi hukumar ta bayyana dalilan da suka haifar da wannan babban bambanci, tare da fayyace matakan da ta ɗauka domin tabbatar da cewa karɓar basussukan gwamnati na tafiya daidai da tsare-tsaren kuɗaɗen da aka amince da su.
Hukumar DMO ce ke da alhakin kula da basussukan Nijeriya, ciki har da karɓar bashin cikin gida da na ƙasashen waje, biyan kuɗaɗen ruwa da sauran kuɗaɗen hidimar bashi, da kuma aiwatar da manufofin gwamnati kan tafiyar da basussuka. Ayyukan hukumar suna da muhimmanci wajen samar da kuɗaɗen gudanar da ayyukan gwamnatin tarayya da kuma kula da nauyin basussukan da ƙasar ke ɗauke da su.
A nata ɓangaren, ana sa ran Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Nijeriya (TCN) zai yi bayani kan zargin kasa karɓo naira biliyan 446.70 daga cikin naira biliyan 882.75 da wasu hukumomi da cibiyoyin gwamnati suka riƙe wa Gwamnatin Tarayya. Kuɗaɗen sun ƙunshi basussukan da ake zargin wasu hukumomin gwamnati da cibiyoyi ke bin gwamnati. Saboda haka, kwamitin zai nemi ƙarin bayani kan ƙoƙarin da TCN ta yi na karɓo kuɗaɗen da kuma dalilan da suka sa aka bar wani kaso mai yawa ba tare da an biya ba.
Wannan zaman sauraron bayanan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da dukiyar jama’a, bin ƙa’idojin kuɗaɗe da kuma karɓo kuɗaɗen gwamnati da suka maƙale a hannun waɗanda ake bin bashi.
