An kama mutane biyar a Ribas da Abiya bisa zargin hannu a sace ‘yan hidimar ƙasa 20

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS), sojoji da ‘yan sanda sun yi nasarar kama wasu mutane guda biyar da ake zargin ‘yan dabar wasu ɓarayi ne bisa zargin su da hannu da garkuwa da ‘yan hidimar ƙasa (NYSC) 20 a Jihar Imo a ranar da Nijeriya ta cika shekaru 66 da samun ‘yancin kai.

Haka kuma, wasu ‘yan dabar su biyar sun tsere ɗauke da raunukan harbin bindiga, lamarin da ya haifar da jami’an sun ɗauki matakin farauto su.

Rahotanni sun bayyana cewa, an kama ‘yan bindigar ne bisa amfani da wasu bayan sirri daga jami’in tsaro a jihohin Ribas da Abia, saidai an samu bambanci akan adadin waɗanda suka tsere yayin atisayen.

Majiyoyin tsaro sun ce an gudanar da jerin atisayen ne a tsakanin ranakun 10 da 14 ga Oktoba a Fatakwal, Ribas da Ƙaramar Hukumar Aba ta Kudu a jihar Abia.

A kwanakin baya ne wasu ‘yan bindiga suka sace ‘yan hidimar ƙasa guda 20 akan hanyar Owerri zuwa Onitsha a Jihar Imo, a lokacin da suke tafiya sansanonin karɓar horo na NYSC daga Ibadan a Jihar Oyo zuwa jihohin Abia da Akwa-Ibom. Daga bisani an ceto su a ranar 7 ga Oktoba, 2026 yayin wani atisayen haɗakar jami’an tsaro a wani yanki na ƙauyen Amakohia Ubi.

Waɗannan atisaye sun nuna samun gagarumar nasara a ƙoƙarin da hukumomin tsaro suke yi wajen farauto masu hannu a ɗanyen aikin, lalata hanyoyin aikata miyagun laifuka musamman ga masu hannu a garkuwar da gurfanar da su domin su fuskanci hukuncin doka.

By Babaji

Leave a Reply