
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun tsaro a Arewa maso Yammacin Nijeriya, sun yi nasarar ceto mutane 27 da aka yi garkuwa da su, ciki har da wani jaririn wata shida bayan musayar wuta da ‘yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Sabuwa da ke Jihar Katsina.
Wannan al’amari ya biyo bayan samun wani kiran gaggawa ga jami’an tsaro daga mazauna ƙauyen Gamji da misalin ƙarfe 12:25 na rana a ranar Juma’a, a cewar wallafar ƙwararren masanin harkar tsaro, Zagazola Makama.
Hakan ya sa aka hanzarta tura sojoji zuwa yankin, amma ‘yan ta’addar sun tsere zuwa bayan gari gabanin isar dakarun ƙauyen. Don haka sai suka bazama zuwa ƙauyen Gangare ta yankin Kamba, inda suka yi arangama da tsararrun ‘yan bindigar da misalin ƙarfe 6:05 na yammacin. A cewar wallafar, sojojin sun yi ba-takashi da ‘yan bindigar ɗauke da makamai masu ƙarfi, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa cikin daji.
Binciken da aka gudanar daga bisani ya taimaka wajen ceto baki ɗaya mutane 27 da aka yi awon-gaba da su, waɗanda suka haɗa da maza 15 da mata 12, har da jaririn wata shida, kamar yadda Makama ya bayyana. Bayan haka ne sojoji suka damƙa su ga Mai garin Gamji, Alhaji Falalu Suleiman bayan sun gudanar da wasu bincike akansu.
Haka kuma, an ruwaito cewa babu rahoton mutuwa ko jikkata daga ɓangaren sojojin, yayin da kuma ba a gano adadin waɗanda suka rasu ko raunata ba daga cikin ‘yan bindigar. Kazalika, Makama ya ce dakarun tsaro sun cigaba da sintiri a yankin da kewayensa domin bayar da kariya ga wasu ayyukan ‘yan ta’adda, taƙaice zirga-zirgar ‘yan bindiga da inganta tsaron mazauna.
