‘Tinubu kake wa aiki’, ADC ta caccaki Kwankwaso kan kiran Atiku ya janye takara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Jam’iyyar African Democratic Congress ADC-PCC, ya yi tir da kalaman abokin tafiyar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, bisa kiransa ga tsohon Maitaimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da ya janye ƙararsa.

Daraktan hulɗa da jama’ar ADC-PCC, Kola Ologbondiyan ya bayyana waɗannan kalamai da aka jingina wa Kwankwaso a matsayin wakiltar kai kuma da yunƙurin isar da manufofin siyasar Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin babban zaɓen 2027.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 16 ga Oktoba, 2026, Ologbondiyan ya ce yana magana ne kan hirar da aka yi da Kwankwaso a gidan talabijin na Channels, inda ya zargi tsohon gwamnan na Jihar Kano da mayar da hankali kan ‘yan adawa a madadin ƙalubalantar gwamnatin Tinubu, wadda a cewarsa, ‘yan Nijeriya suke ƙoƙarin kayarwa a zaɓe mai zuwa.

Ologbondiyan, ya ci alwashin cewa Atiku zai ya yi nasara a Jihar Kano, mahaifar Kwankwaso a zaɓen shugaban ƙasa ko da kuwa bai samu goyon bayan dan Kanon ba. Ya ce, matsin rayuwa, yunwa, talauci da rashin tsaro da ‘yan Nijeriya suke fuskanta sune za su yi la’akari da hukuncin da za su yanke a zaɓen.

Kakakin jam’iyyar ya ƙara da cewa, kamata ya yi a ce Kwankwaso ya gina adawarsa akan gwamnati mai ci a madadin sukar wani ɗan adawa, yana mai ƙalubalantarsa akan ayyukansa suna amfanar da jam’iyya mai mulki APC a maimakon yadda jam’iyyarsa zai kai ga nasara a zaɓen na 2027.

By Babaji

Leave a Reply