
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Juma’a Sakatariyar Fadar White House a Amurka, Katie Zacharia, ta ajiye muƙamin bayan ƙasa da mako guda da fara babban aikin. Hakan ya biyo bayan waɗansu jerin kurakurai da suka hura wutar kawar da hankalin mai gidanta Shugaba Donald Trump daga gudanar da wasu harkokin gwamnati.
An fitar da wani rubutu da fari mai ɗauke da saƙon cewa Shugaba Trump ya shirya ganin sabuwar kakakinsa yayin sukar da ake mata cewa ta yi ƙaryar cewa ita lauya ce da kuma shan suka daga masana harkokin yaɗa labarai.
Zacharia ta fara aiki ne kwanaki biyar da suka gabata bayan maye gurbin Karoline Leavitt, wadda ta taimaka wa Trump inganta harkokin ɗaukar rahotannin White House ta yadda an samu ƙarin wasu kafafen labarai da ke taimaka wa yaƙar kafafen labarai masu sukar manufofin gwamnati da waus muhimman al’amuran gwamnatinsa.
Ta fara aikin ne da wata hirar minti 15 cikin yanayi na jinkirin karanto abin da ta kira da “cimma manufofi da dama” na Shugaba Trump, inda ta amsa tambayoyi uku kaɗai daga ‘yan jarida. Al’ummar ƙasar sun fara cece-kuce akan Katie ne bayan an gano cewa iƙirarin nata na zama lauya ba gaskiya ba ne.
Wannan tayar da ƙura ya haifar da tsaiko ga Trump mai shekaru 80 yayin da yake kewaye sassan ƙasar domin ƙarfafa ‘yan takarar jam’iyyar Republican, gabanin zaɓen ‘yan majalisa na zaɓukan tsakiyar wa’adin mulki da za a yi a ranar 3 ga Nuwamba.
