RTEAN Singa ta koka kan lalacewar hanyoyi da cin zarafin direbobi

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Shugaban ƙungiyar Masu Motocin Haya ta Nijeriya (RTEAN), reshen Kasuwar Singa da ke Kano, Kwamared Yakub Haruna, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta gyara manyan hanyoyin ƙasar nan domin sauƙaƙa zirga-zirgar ababen hawa da rage wahalhalun da direbobi ke fuskanta.

Ya bayyana cewa lalacewar hanyoyi ta ƙara tsawaita lokacin da ake ɗauka wajen yin tafiye-tafiye, inda ya ce hanyar Kano zuwa Gwarzo, wadda a baya ake iya bi cikin sa’o’i biyu zuwa uku, yanzu tana ɗaukar sa’o’i huɗu zuwa biyar saboda lalacewarta.

Ya ƙara da cewa, wasu hanyoyin da a da ake iya bi cikin sa’o’i biyar, yanzu sai an shafe sa’o’i bakwai zuwa goma kafin a isa inda ake so, lamarin da ke jefa matafiya da direbobi cikin aarin wahala.

Kwamared Yakub Haruna ya ce hanyoyin Kano zuwa Abuja da Kano zuwa Maiduguri na daga cikin hanyoyin da za a iya tafiya da ɗan sauƙi idan aka kwatanta da sauran hanyoyin da suka lalace matuƙa.

A cewarsa, lalacewar hanyoyin na haifar da ƙarin kuɗin man fetur da kuma yawan lalacewar motoci, wanda ke ƙara wa direbobi nauyin kashe kuɗi tare da shafar kuɗin shiga da suke samu.

Ya kuma yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa matakin rage farashin man fetur na tsawon kwanaki 30, amma ya bayyana cewa da an rage farashin da kashi 40 cikin 100, da hakan ya fi sauƙaƙa wa masu ababen hawa da sauran al’umma.

A wani ɓangare na koken nasa, shugaban RTEAN ɗin ya nuna damuwa kan ci gaba da cin zarafin direbobi da wasu jami’an tsaro ke yi, duk da matakan da aka ɗauka na rage shingayen binciken da ba su da inganci a wasu sassan kudancin ƙasar nan.

Ya ce har yanzu wasu jami’an tsaro na tilasta wa direbobi bayar da kuɗi daga naira 200 zuwa naira 500, lamarin da ya ce bai dace ba.

Kwamared Yakub Haruna ya jaddada cewa kowane ɗan ƙasa na da ’yancin zirga-zirga cikin walwala, don haka bai kamata a riƙa tsangwamar direbobi ko tilasta musu bayar da kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.

Ya kuma yi kira ga direbobi da su riƙa bin dokokin hanya da ƙa’idojin zirga-zirga a duk inda suke, domin tabbatar da tsaro da kauce wa haɗurra yayin gudanar da ayyukansu.

By ukarofi

Leave a Reply