Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta buƙaci kamfanonin haɗa motoci na cikin gida da su aara yawan motocin da suke ƙerawa, inganta ingancinsu da kuma inganta ayyukan gyara da kula da motoci bayan sayarwa, yayin da take ƙarfafa aiwatar da manufar ‘Nigeria First’ ta fifita kayayyakin da aka ƙera a Nijeriya wajen sayayya da hukumomin gwamnati ke yi.
Babban Daraktan Hukumar Bunƙasa Tsarin ƙera Motoci ta ƙasa (NADDC), Oluwemimo Joseph Osanipin, ne ya bayyana hakan a Abuja, inda ya ce kamfanonin hada motoci da ke Nijeriya na da ƙarfin samar da motoci 370,520 a duk shekara. Osanipin ya ce fifita kamfanonin cikin gida wajen sayayyar gwamnati zai samar da guraben ayyukan yi, rage shigo da motoci daga ƙasashen waje tare da bunƙasa ƙera kayayyakin haɗa motoci a cikin gida.
Ya bayyana cewa ana sauya tsarin aiwatar da manufar Fifita Nijeriya, wato Nigeria First ta yadda duk motocin da ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnati za su saya, ciki har da motocin gudanar da ayyukan gwamnati, za a samo su ne kawai daga kamfanonin haɗa motoci da aka ba lasisi a Nijeriya ko dillalan da suka amince da su. Ya ce, “Muna sauya yadda ake aiwatar da manufar Nigeria First gaba ɗaya. Dole ne a sayo duk motocin da ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnati za su saya, har da motocin da ake amfani da su wajen gudanar da ayyuka, daga kamfanonin haɗa motoci masu lasisi a cikin gida ko dillalan da suka amince da su kawai. Haka kuma, babu wata ma’aikata ko hukuma da za ta sayi motar da aka haɗa a ƙasar waje sai ta gabatar da hujjar cewa babu irin motar da ake buƙata da za a iya samu a cikin gida, sannan ta sami amincewar Shugaban ƙasa kai tsaye.”
Osanipin ya ƙara da cewa, duk motar da aka samar wa gwamnati dole ne ta kasance tana da lambar tantancewa ta musamman, wato ɓehicle Identification Number (ɓIN), wadda za a iya bibiyarta tare da tabbatar da sahihancinta ta hannun NADDC. Ya yi gargaɗin cewa duk wani mai samar da motoci da ya kauce wa tsarin haɗa motoci da aka amince da shi zai fuskanci hukunci nan take, wanda zai iya haɗawa da sanya shi cikin jerin waɗanda aka haramta hulɗa da su da kuma soke lasisinsa.
A ƙarƙashin manufar, dole ne hukumomin gwamnati su sayi motocinsu daga kamfanonin haɗa motoci masu lasisi a Nijeriya ko dillalan da aka amince da su. Duk wata buƙatar sayen motar da aka haɗa a ƙasashen waje za ta buƙaci hujjar cewa babu makamanciyarta a cikin gida, tare da amincewar Shugaban ƙasa. Hukumar Kula da Sayayyar Gwamnati (BPP) ta gargaɗi kamfanonin haɗa motoci na cikin gida cewa za su fuskanci takunkumi idan suka samar da motoci marasa inganci, suka gaza bayar da isasshen tallafin gyara bayan sayarwa ko kuma suka karya ƙa’idojin manufar.
Hukumar ta kuma jaddada cewa duk motocin da aka samar wa gwamnati dole ne su kasance da lambobin tantancewa na musamman da za a iya bibiyarsu, waɗanda NADDC za ta tabbatar da sahihancinsu domin tabbatar da bin sabbin ƙa’idojin sayayyar gwamnati.
Babban Daraktan BPP, Adebowale Adedokun, ya buƙaci masu ƙera motoci da su zuba jari a fannin fasaha, inganta matakan kula da inganci da kuma ayyukan gyara da kulawa da motoci, yayin da Gwamnatin Tarayya ke ƙoƙarin gina masana’antar kera motoci mai gasa a kasuwannin cikin gida da na duniya. Adedokun ya jaddada buƙatar kamfanonin haɗa motoci na cikin gida su inganta motocin da suke samarwa da kuma ayyukan da suke bayarwa bayan sayarwa, domin biyan buƙatun gwamnati a ƙarƙashin manufar Nigeria First.
