Nijeriya ce ta fi samun ƙaruwar talauci a duniya – Majalisar Dinkin Duniya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Nijeriya ce ta fi kowace ƙasa a duniya samun ƙarin mutanen da ke fama da talauci ta fuskoki daban-daban, inda mutum miliyan 17.9 suka faɗa cikin wannan hali tsakanin shekarar 2021 zuwa 2024, kamar yadda rahoton Ma’aunin Talauci ta Fuskoki Daban-daban na Duniya na 2026 ya bayyana.

Rahoton da Shirin Bunƙasa ƙasashe na Majalisar ɗinkin Duniya (UNDP) da Shirin Bincike kan Talauci da Ci gaban Bil Adama na Jami’ar Oxford (OPHI) suka wallafa ranar Litinin, ya nuna cewa Nijeriya ta samu koma-baya a ƙoƙarin rage talauci, bayan da ta samu ci gaba a tsakanin shekarar 2018 da 2021.

Sakamakon binciken ya nuna cewa Nijeriya ta zarce ƙasar Afghanistan, wadda ta samu ƙarin mutum miliyan 5.3 cikin masu fama da talauci a lokacin bincikenta na baya-bayan nan. Wannan ya nuna girman matsalar talauci da ta ƙara ta’azzara a Nijeriya. Rahoton ya ce: “Idan aka duba adadin mutane kai tsaye, Nijeriya ce ta fi kowace ƙasa samun ƙarin mutanen da suka faɗa cikin talauci. Duk da cewa talauci ya ragu a ƙasar tsakanin shekarar 2018 da 2021, a tsakanin 2021 da 2024 mutum miliyan 17.9 suka shiga talauci ta fuskoki daban-daban. Afghanistan ce ta biyo baya da mutum miliyan 5.3.”

Wannan na nufin Nijeriya ce ta fi kowace ƙasa da ake da bayanan da za a iya kwatantawa samun koma-baya mafi girma ta fuskar yawan mutanen da talauci ya shafa. Lamarin ya haifar da damuwa kan taɓarɓarewar yanayin rayuwa da kuma koma-bayan da aka samu a ƙoƙarin rage talauci.

Rahoton ya sanya Nijeriya cikin ƙasashe biyar da suka samu ƙaruwar talauci ta fuskoki daban-daban a lokacin da aka tantance su. Sauran ƙasashen su ne Afghanistan, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Guinea da Kyrgyzstan. A cewar rahoton, ƙarin talauci ya faru ne a Afghanistan tsakanin 2015/2016 da 2022/2023, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tsakanin 2010 da 2018/2019, Guinea tsakanin 2016 da 2018, Kyrgyzstan tsakanin 2018 da 2023, sannan Nijeriya tsakanin 2021 da 2024.

Ma’aunin Talauci ta Fuskoki Daban-daban (MPI) ba ya auna talauci ta hanyar kuɗin shiga kaɗai. Yana duba matsalolin da mutane ke fuskanta wajen samun ilimi, kiwon lafiya, wutar lantarki, ruwan sha, tsaftar muhalli, matsuguni mai inganci da abinci mai gina jiki. Wannan ya bambanta da ma’aunin talauci da ke la’akari da kuɗin shiga ko yawan kuɗin da mutum ko iyali ke kashewa. MPI na tantance matsaloli daban-daban da ke addabar iyalai a lokaci guda, tare da duba tasirinsu ga rayuwarsu.

Ana ɗaukar mutum a matsayin mai fama da talauci ta fuskoki daban-daban idan ya fuskanci matsaloli a aƙalla kashi ɗaya bisa uku na alamomin da ake amfani da su wajen auna lafiya, ilimi da yanayin rayuwa. Wani nazari da aka yi domin kwatanta bayanan shekaru daban-daban ya nuna cewa adadin mutanen da ke fama da wannan nau’in talauci a Nijeriya ya tashi daga kashi 33 cikin 100 a shekarar 2021 zuwa kashi 38.7 a shekarar 2024. Wannan na nufin an samu ƙarin maki 5.7 cikin 100.

Adadin mutanen da abin ya shafa ya ƙaru daga miliyan 72.21 zuwa miliyan 90.07 a wannan lokaci, yayin da ƙimar ma’aunin MPI ta ƙaru daga 0.175 zuwa 0.208, abin da ke nuna cewa yanayin talauci ya ƙara tsananta. Sai dai wani ƙiyasin ƙasa da rahoton ya fitar na shekarar 2024 ya nuna cewa mutum miliyan 113.32 ne ke fama da talauci ta fuskoki daban-daban a Nijeriya, adadin da ya kai kashi 48.7 cikin 100 na al’ummar ƙasar.

Rahoton ya bayyana cewa wannan ƙiyasi ya dogara ne da sabon binciken ƙasa, ba tare da gyare-gyaren da aka yi wa bayanan baya domin kwatanta shekarun da suka gabata ba. Saboda haka, ya bambanta da adadin da aka samu a nazarin da ya daidaita bayanan tarihi. Haka kuma, rahoton ya nuna cewa kashi 28.7 cikin 100 na ’yan Nijeriya na fama da matsanancin talauci ta fuskoki daban-daban, yayin da kashi 18.1 ke cikin haɗarin faɗawa cikin irin wannan talauci. Rahoton ya ƙara da cewa, “A Nijeriya, talauci ya ragu tsakanin 2018 da 2021, amma ya sake ƙaruwa tsakanin 2021 da 2024.”

Binciken ya nuna cewa akwai bambanci sosai tsakanin jihohin Nijeriya wajen yawan mutanen da talauci ya shafa da kuma irin matsalolin da suke fuskanta.

Jihohin Kebbi, Yobe da Sokoto na cikin waɗanda suka fi fama da talauci ta fuskoki daban-daban, yayin da Jihar Legas ta samu mafi ƙarancin ƙimar MPI. Rahoton ya kuma nuna cewa hatta yankunan da ke fama da talauci mai tsanani na iya bambanta wajen irin matsalolin da suka fi addabarsu, duk da cewa kimar talaucinsu na iya zama kusan ɗaya. A matsayin misali, rahoton ya kwatanta jihohin Yobe da Sokoto, inda ya ce duk da cewa kimar MPI ɗinsu ta yi kama, matsalolin rashin isasshen abinci mai gina jiki da yawan mace-macen yara sun fi taimakawa wajen ƙara talauci a Yobe.

A Sokoto kuwa, rashin isasshen ruwan sha da wutar lantarki sun fi taka rawa wajen tsananta talauci. Rahoton ya jaddada cewa fahimtar irin waɗannan bambance-bambance na da muhimmanci wajen tsara matakan rage talauci da suka dace da buƙatun kowace al’umma, maimakon amfani da tsari guda ga dukkan yankuna. A matakin duniya, rahoton ya ƙiyasta cewa mutum biliyan 1.2, kwatankwacin kashi 18.9 cikin 100 na al’ummar da binciken ya ƙunsa, na rayuwa cikin matsanancin talauci ta fuskoki daban-daban. Daga cikinsu, mutum miliyan 534 na fama da matsanancin talauci, yayin da wasu miliyan 952 ke cikin haɗarin faɗawa cikin wannan hali.

Nahiyar Afirka da ke kudancin Sahara ce ke da mafi yawan mutanen da talauci ya shafa, inda adadinsu ya kai miliyan 616, sama da rabin jimillar mutanen da ke fama da talauci a duniya. Binciken ya kuma nuna cewa mutum miliyan 617 daga cikin masu fama da talauci ta fuskoki daban-daban a duniya yara ne ‘yan ƙasa da shekara 18. Wannan na nuna cewa yara na ɗaukar babban kaso na nauyin matsalolin talauci.

By ukarofi

Leave a Reply