Majalisar Wakilai ta gayyaci minista da akanta janar kan bashin biliyan N75 na hukumar UBEC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kwamitin Majalisar Wakilai akan Kuɗaɗen Al’umma, ya gayyaci Ministan Kuɗi Taiwo Oyedele da Akanta Janar na Ƙasa (AGF), Shamseldeen Ogunjimi, kan batun bashin Naira biliyan 75 da ake bin Hukumar Ilimin Bai-Ɗaya (UBEC).

A wata sanarwa da aka aike wa jaridar TheCable a ranar Asabar, an umarci Oyedele da Ogunjimi da su bayyana a gaban kwamitin a ranar Alhamis, 22 ga Oktoba, 2026 domin bayar da ba’asi akan lokacin za a biya bashin na UBEC da wasu muhimman al’amura kan batun.

Wannan ya biyo bayan kokawa da mambobin kwamitin suka yi bisa ragewa da aro kuɗaɗen muhimman hukumomin gwamnati ba tare da cikakken tsari, sharaɗin biya, ko yarjejeniyar biya ba.

Kwamitin ya nace akan sai an dakatar da yawan rage kuɗaɗe daga asusun hukumar, yana mai cewa wajibi ne dukkan wani tsarin kuɗi tsakanin gwamnati da gwamnati ya samar da gamsashshen bayani kan sharuɗɗa da ƙa’idojin gudanarwa. Haka kuma, ya ce dole ne dukkan hukumomin da za su aro kuɗi, su yi bayanin yadda za biya da lokacin da za a kammala biyan a hukumance tare da tabbatar da cika alƙawari.

Mataimakin Shugaban kwamitin, Jeremiah Umaru ya koka kan tasirin bashi a fannin ilimin matakin farko, yana mai bayyana shigar UBEC cikin harkokin ilimi a matsayin muhimmin ci-gaban ƙasa, don haka wajibi a samar da hanyoyin kula da dokokin gudanarwa bisa tsari domin amfanin al’umma da ma ƙasa baki ɗaya.

By Babaji

Leave a Reply