Yadda Shell ya sayar da kasuwancinsa na iskar gas a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanin mai na Shell Petroleum B.ɓ. ya sanya hannu kan yarjejeniyar sayar da dukkan hannun jarinsa a rukunin kamfanonin Shell Nigeria Gas ga ɓaaris Energy Limited, wani kamfanin makamashi na Nijeriya.

Kamfanin Shell ya bayyana cewa yarjejeniyar za ta bai wa ɓaaris Energy damar karɓar ragamar kasuwancinsa na iskar gas a cikin Nijeriya. A cikin wata sanarwa da Shell ta fitar ranar Talata, kamfanin ya ce yarjejeniyar za ta shafi Shell Nigeria Gas Holding B.ɓ., wanda aka kafa a shekarar 2019, kuma yake riƙe da kusan dukkan hannun jarin kamfanin SNG Limited, ban da guda ɗaya.

Sai dai kammala yarjejeniyar ya danganta da cika ƙa’idojin hukumomin da abin ya shafa da kuma samun amincewarsu. Da take tsokaci kan yarjejeniyar, shugabar Shell a Nijeriya, Elohor Aiboni, ta ce Shell Nigeria Gas ta shafe sama da shekaru 25 tana samar da ayyukan rarraba iskar gas ga masana’antu da ’yan kasuwa a ƙasar, sakamakon ƙwarewa da jajircewar ma’aikatanta. Ta ce, “Muna ganin wannan yarjejeniya za ta samar da ingantaccen tushe da zai taimaka wa kasuwancin wajen shiga sabon mataki na ci gabansa a ƙarƙashin sabon mai shi. Shell za ta ci gaba da mayar da hankali kan muhimman ayyukanta na hako mai a zurfin teku da kuma harkokin iskar gas a Nijeriya.”

A cewar sanarwar, rukunin kamfanonin SNG zai ci gaba da kasancewa ƙarƙashin mallakar Shell tare da gudanar da ayyukansa da yi wa abokan hulɗarsa hidima kamar yadda aka saba, har sai an kammala cinikin. Shell ya ce, sayar da hannun jarin ya yi daidai da dabarunta na rage yawan sassan kasuwancinta domin mayar da hankali kan fannoni da take da ƙwarewa da fifiko a kansu.

Kamfanin ya ƙara da cewa, ci gaba da mayar da hankali kan ayyukan haƙo mai a zurfin teku da haɗaɗɗun ayyukan iskar gas a Nijeriya, ciki har da hannun jarinsa a kamfanin Nigeria LNG, wani ɓangare ne na wannan dabara. Sanarwar ta kuma bayyana cewa SNG ba ta gudanar da ayyukan hako iskar gas daga rijiyoyi, samar da iskar gas mai sanyi da ake jigilarwa a matsayin ruwa (LNG), ko cinikin iskar gas tsakanin ƙasashe.

An kafa kamfanin Shell Nigeria Gas a 1998, kuma yana samar da gas ga masana’antu da ’yan kasuwa. Haka kuma, kamfanin yana da hanyar bututun iskar gas mai tsawon kusan kilomita 170 da ta ratsa jihohin Ogun, Abia da Ribas.

By ukarofi

Leave a Reply