Bayan shekaru 15, Ektaa Kapoor ta tabbatar da shirin fim ɗin The Dirty Picture 2

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Bayan shafe shekaru 15 tun bayan fitowar fim ɗin The Dirty Picture, fitacciyar mai shirya fina-finai a Indiya, Ektaa Kapoor, ta tabbatar da cewa tana shirin fitar da kashi na biyu na fim ɗin da ya yi fice a shekarar 2011, amma ta bar masu kallon fina-finai cikin jiran sanin jarumar da za ta taka muhimmiyar rawa a sabon aikin.

Ektaa ta bayyana shirinta ne a wata tattaunawa da ta yi a shirin hira na Ranveer Allahbadia, inda ta ce ta dade tana tunanin ci gaba da labarin fim ɗin, amma sai da ta samu wani sabon labari da take ganin ya dace ta gabatar wa masu kallo kafin ta yanke shawarar ci gaba da aikin.

Fim ɗin farko, wanda Vidya Balan ta taka muhimmiyar rawa a cikinsa, ya ba da labarin rayuwar wata jarumar fina-finan Indiya da kuma ƙalubalen da take fuskanta a cikin masana’antar nishaɗi. Vidya ta taka rawar da ta jawo mata yabo sosai, har ta lashe lambar yabo ta ƙasa ta Indiya a matsayin fitacciyar jaruma.

Sai dai, duk da tabbatar da cewa za a shirya sabon fim ɗin, Ektaa ba ta bayyana sunan jarumar da za ta fito a cikinsa ba, ko waɗanda za su taka sauran manyan rawar, haka kuma ba ta bayyana ranar da za a fitar da shi ba.

Abin da ya fi jan hankali shi ne yadda mai shirya fim ɗin ta bayyana cewa sabon aikin ba wai kawai za a yi shi ne saboda nasarar fim ɗin farko ba, a’a, tana da wani sabon labari da take son isar wa masu kallo.

Wannan ya sa masu bibiyar harkar fina-finan Bollywood ke jiran ƙarin bayani, musamman ganin yadda fim ɗin farko ya bar tarihi a masana’antar tare da nuna yadda labarin rayuwar mace zai iya zama babban jigon fim mai jan hankali.

By ukarofi

Leave a Reply