Nishadi

Aminu Ala ya yi babban rashi

Aminu Ala ya yi babban rashi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Allah Ya yi wa Hajiya Bilkisu Sharif Adam, mahaifiyar shahararren mawaƙin Hausa Aminu Ladan Abubakar (Alan waƙa) rasuwa. Marigayiyar ta rasu tana da shekara 70 a duniya, ta rasu ta bar 'ya'ya biyu, Aminu Ladan Abubakar da kuma 'yar'uwarsa Khadija. Da safiyar wannan Talatar misalin ƙarfe 9 ake sa ran gudanar da jana'izar ta a gidansa da ke Maidile a birnin Kano.
Read More
Allah Ya jiƙan Hajiya Umma Ali

Allah Ya jiƙan Hajiya Umma Ali

Daga IBRAHIM MANDAWARI A ranar Lahadin ta gabata, 01/08/2021, Hajiya Umma Ali ta amsa kiran Mahalicci, wato Allah ya karɓi ranta bayan gajeriyar rashin lafiya.Babu shakka masana'antar shirya fina-finan Hausa da ma al'ummar musulmi bakiɗaya mun yi babban rashi wannan baiwar Allah. Ta shigo wannan masana'anta tun wajajen shekarar 1998 kuma ta fara shirya fim tun a wannan lokaci da sunan Kamfaninta, wato UMMA ALI VENTURES. Haka kuma, sakamakon kyakkyawar mu'ala ya sanya kusan dukkan Jarumai a wancan lokaci suka mayar da gidanta tamkar gidajensu na haihuwa. Hajiya Umma Ali ta raini maza da mata na wannan masana'anta ta hanyar…
Read More
Rayuwar ‘yan wasan kwaikwayo a Arewa daga Ibrahim Mandawari

Rayuwar ‘yan wasan kwaikwayo a Arewa daga Ibrahim Mandawari

Daga IBRAHIM MANDAWARI Kamar yadda wasu suka sani wasan kwaikwayo a Arewacin Nijeriya ya samo asali ne tun lokacin Mulkin Mallaka, wato lokacin da Turawan Ingila ke mulkin wannan ƙasa tamu Nijeriya. Hakan kuwa ya samo asali ne daga fuskoki guda uku; wato: Fuska ta ɗaya, wasannin kwaikwayo domin wayar da kai ga talakawa a fannoni daban-daban na rayuwa, misali wayar da kai a kan bunƙasa aikin gona musamman noman gyaɗa da auduga (Shirin Baban Larai), da kuma shiri a kan wayar da kai domin a ƙyale mata masu ciki su dinga halartar ƙananan asibitoci don haihuwa (Mama Learns a…
Read More
Abinda ya haɗa ni rigima da Baturen ‘Yan Sandan Hotoro – Mansurah Isah

Abinda ya haɗa ni rigima da Baturen ‘Yan Sandan Hotoro – Mansurah Isah

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano A sati biyun da su ka gabata ne tsohuwar jaruma Mansurah Isah ta yi wata sanarwar ɓatan wata yarinya wadda har ta zargi Baturen 'Yan Sanda na Hotoro da cewar ya na neman ya ɓoye gaskiyar abin da ya faru, kuma hakan ya sa maganar ta yi tsayi har ta je ga ofishin Kwamishinan 'Yan sanda na Jihar Kano. Don haka ne muka nemi jin ta bakin Mansurah Isah don jin yadda maganar ta samo asali. Wakilin Manhaja a Kano ya samu damar tattaunawa da Mansura don kawo wa masu karatun mu gaskiyar zancen, domin…
Read More
Mansurah Isah ta ƙalubalanci DPO kan ƙin sauraron ƙorafin fyaɗe da suka kai masa

Mansurah Isah ta ƙalubalanci DPO kan ƙin sauraron ƙorafin fyaɗe da suka kai masa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, Mansurah Isah, ta ƙalubalanci DPO na ofishin 'yan sanda na Hotoro a jihar Kano da ya yi aikinsa yadda ya kamata saboda a cewarta jama'a na kallonsa. Da alama dai kalaman Mansurah ba su rasa nasaba da yadda ɓatagarai ke lalata rayuwar ƙananan yara a jihar Kano ta hanyar yi musu fyaɗe da sauransu, inda ta ce iyaye da yawa na nan suna kuka saboda yadda aka ɓata wa yaransu rayuwa bayan an sace yaran an kuma sako su. Mansurah ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram a cikin wannan…
Read More
Silar shiga ta cikin marubutan ‘Labarina’ – Saddiƙa Habib Abba

Silar shiga ta cikin marubutan ‘Labarina’ – Saddiƙa Habib Abba

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano Rubutu wani abu ne da masu yin sa su ke samun damar isar da sakon su ga Jama'a yadda za su yaɗa manufar su walau ta ɓangaren addini ko kuma ɓangaren al'ada, da ma fanoni daban daban na rayuwa. Saddiƙa Habib Abba tana cikin Marubutan wannan lokacin da su ke da burin faɗakar da jama'a ta ɓangaren zamantakewar rayuwar su ta yau da kullum, kuma tana ɗaya daga cikin marubutan da Allah ya yi wa baiwar yin rubutun ta kowanne ɓangare. Domin kuwa marubuciyar labarin Hikaya ce, kuma marubuciya ce a kan al'amuran yau da…
Read More
Me ya kawo rabuwar auren Sani Danja da Mansurah Isah?

Me ya kawo rabuwar auren Sani Danja da Mansurah Isah?

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano A 'yan kwanakin nan babu abin da ya fi ɗaukar hankalin mutane kamar labarin rabuwar auren Sani Danja da Matarsa Mansurah Isah. Labarin dai ya fara ne tun daga ranar Larabar da ta gabata, in da ita Mansurah ta bada sanarwa a shafinta na Instagram cewa ba su tare da mijinta Sani Danja. To sai dai ba ta yi wani ƙarin bayani ba, sannan kuma bayan ɗan wani lokaci da saka labarin sai ta yi sauri da goge shi. Bayan wannan kuma ba ta ƙara cewa komai ba a kan lamarin. Wakilinmu ya yi ƙoƙarin…
Read More
Na yi da-na-sanin rera waƙar Abubakar Ladan, Cewar Aminu ALA

Na yi da-na-sanin rera waƙar Abubakar Ladan, Cewar Aminu ALA

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Ɗaukar waƙar wani mawaƙi rubutacciya a rera ta ba wani sabon abu ba ne a fagen waƙa a duniya. Don haka ne ma ake samun wasu mawaƙan ko dai su saya ko su nemi izinin rera wata rubutacciyar waƙa da wani mawaƙi ya zauna ya tsara. Irin wannan salo ne fitaccen Mawaƙi Alhaji (Dakta) Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya yi amfani da waƙar 'Afrika' ta Marigayi Malam Abubakar Ladan Zariya, inda ya rera ta a salo na zamani tare da kayan kiɗa na zamani da nufin zamanantar da waƙar. To, sai dai bayan fitar waƙar…
Read More