Ƙungiyar matasa ta naɗa Ado Ahmad muƙamin ‘Sarkin Mawallafan Arewa’

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Arewa Youth And Women For Change ta naɗa shahararren marubucin nan, Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino MON, daga Jihar Kano a matsayin ‘Sarkin Mawallafan Arewa na Farko’ kuma ‘Jakadan Zaman Lafiyar Arewa’.

Bayanin naɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun Babbar Sakatariyar Ƙungiyar, Ambasada Sadiya Ahmed Birniwa.

Ƙungiyar ta ce ta naɗa Ado wannan muƙamin ne duba da irin gudunmawar da yake bayarwa ga cigaban al’umma, musamman ga rayuwar mata da matasa.

Ta ƙara da cewa, sai da ta yi nazari mai zurfi tare da tantance wasu ɗaiɗaikun jama’a ta hanyar duba rawar da suke takawa a cikin al’umma wanda a ƙarshe ta ga Alhaji Ado ne ya fi cancanta da wannan muƙami.

A cewar ƙungiyar, bikin naɗin da karramawar zai gudana ne a Yankari Game Reserve da ke Bauchi yayin bikinta na baje kolin al’adun gargajiya na ƙasa da ƙasa na bana da zai gudana a Borno.

A ƙarshe, ƙungiyar ta taya Ado murnar samun wannan muƙami, tare da yi masa fatan nasara a harkokinsa.