Dala ta sake shan kaye a hannun Naira, Dala 1 ta koma N1000

Daga BASHIR ISAH

Kawo yanzu, Dalar Amurka na ci gaba da shan kashi a hannun Naira ta Nijeriya.

Bayanai sun ce a wannan Litinin ɗin, an sayar da Dala 1 kan N1000 a kasuwar canji.

Idan za a iya tunawa, a Litinin ta makon jiya Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya saida wa ‘yan canji (BDC) Dala miliyan $15.88 a kan N1,101 ga kowace Dala 1.

‘Yan Nijeriya na ci gaba da fatan ganin Naira ta yi wa Dala rugugu ko sa samu sauƙin tsadar rayuwar da ake alƙanta ta da tashin Dala.