
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya yi kira ga a ɗauki matakai masu ƙarfi domin bai wa mutane masu nakasa kariya a zaɓukan 2027 da ke tafe don tabbatar da tsare gaskiya da adalci kan ‘yancin masu zaɓe.
Da yake jawabi a ranar Juma’a yayin wata ganawa da jami’an ƙungiyar TAF Africa ta jami’an Rundunar ‘Yan sanda Nijeriya (NPF) a Abuja, Amupitan ya ce wulaƙanci da rashin damar zuwa rumfunan zaɓe ka iya haramta wa ‘yan ƙasa da suka cancanta yin amfani da ‘yancin da dokar ƙasa ta ba su.
Shugaban na INEC ya ce sahihancin zaɓe ya dogara ne da ko kowane ɗan ƙasa ya samu damar yin zaɓe cikin ‘yanci, bisa aminci kuma ba tare da nuna masa wariya ba. “Ba za a kira zaɓe da bai wa kowane ɓangare dama ba muddin aka wulaƙanta mutane masu nakasa ko wasu marasa galihu ko suka fuskanci matsalolin rashin ko kuma wasu ƙalubale da ka iya katange su daga aiwatar da ‘yancinsu,” inji shi.
Ya bayyana cewa, akwai buƙatar a ɗauki matakan gaggawa kan lamuran tsaro musamman akan masu nakasa ta bayar da horo ga ‘yan sanda domin jagorantar aikin tabbatar da bai wa irin mutanen dukkan kulawar da ta dace yayin zaɓukan.
Ya ƙara da cewa, ya dace shirin tsaro ya ƙunshi baki ɗaya lamuran gudanar da zaɓe, ciki har da rajistar masu zaɓe, yaƙin neman zaɓen siyasa, gangami, lokacin kaɗa ƙuri’a da bayan haka, yana mai kira ga jami’an hukumomin tsaro da su tabbatar da bayar da dukkan agajin da ake buƙata tare da kare sirrinsu musamman kan ‘yancin sakaye ƙuri’a bisa nuna ƙwarewar aiki.
