Yanzu-yanzu: An garzaya da matar da ta shigo Nijeriya da Ebola Switzerland

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Litinin Ministan Lafiya da Walwalar Al’umma, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya tabbatar da cewa an fitar da mai ɗauke da cutar Ebola da ta shigo da ita Nijeriya zuwa ƙasar Switzerland da ke Nahiyar Turai.

Farfesa Pate ya bayyana haka ne a wata wallafa a shafinsa na X, inda ya ce, matar, wadda ta soma samun sauƙi, tana nan a hayyacinta sannan an fita da ita ne tare da mijinta, wanda babu alamar rashin lafiya a tare da shi.

Ministan, kamar yadda ya rubuta: “Ina mai tabbatar da cewa, da amincewata a safiyarnan, an fitar da mutum na farko da ya shigo Nijeriya da cutar Ebola zuwa ƙasar Switzerland daga Abuja. Mara lafiyar ta samu sauƙi sosai kuma tana cikin hayyacinta, sannan sakamakon gwajin lafiyarta ya nuna madaidaicin mataki.”

Saidai, ya ce kasancewar matar ta soma warkewa, hakan ba shi yake nuna cewa a yanzu babu cutar a tare da ita, inda ya ƙara da cewa an ɗauki muhimman matakai gabanin fita da ita ƙasar wajen. “Za mu bayar da ba’asin halin da ake ciki da rana bayan maras lafiyar da mijin nata sun isa inda suka dosa lafiya,” inji shi.

Ministan ya kuma ce, gwamnatin tarayya tana ɗaukar matakan lafiyar al’umma wajen cigaba da tabbatar da daƙile yaɗuwar cutar da aka shigo ita cikin ƙasar. Akan haka ne ya kirayi ‘yan Nijeriya da su kasance masu lura da sanya ido tare da cigaba da dogara da labaran da ake yaɗawa kan al’amarin ta sahihan kafafen yaɗa labarai tare da ƙaurace wa amfani da labaran bogi.

Wannan dai na zuwa ne bayan da a ranar Lahadi Cibiyar Kula da bayar da Kariya ga Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) ta fitar da rahoton cewa, adadin waɗanda aka yi wa gwaji masu alaƙa da cutar Ebola a Nijeriya ya kai 53 a watan Oktoban 2026. Ta ce, waɗanda hakan ya shafa sun haɗa da ma’aikatan lafiya da ma’aikatan cikin gida da matar wannan mutumin.

By Babaji

Leave a Reply