Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Littafi abu ne mai muhimmanci ga rayuwar ɗan adam, duba da yadda littafi ke taimakawa wajen adana muhimman bayanai da labarai da suka jiɓanci harkokin rayuwa daban-daban, kama daga tarihi, bayanan da suka shafi harkokin kimiyya da fasaha da tattalin arziki, tarihin ƙasa da muhimman mutane da al’adu da sauransu.
Ranar littafi da kare ‘yancin mallakar fasaha ta duniya ta samo asali ne tun a shekarar 1616 lokacin da aka yi rashin wasu fitattun marubuta irinsu Cervants, da Sharkspare da Inca Garcilaso de La vega. Kana a shekarar ce kuma aka samu wanzuwar wasu fitattun marubuta kamar Maurice Droun da Haldor K Laxness, da Vladimir Nabokov, da Josep Pla da Manuel Mejia Vallejo da sauransu.
A ranar 23 ga watan Afrilun shekarar 1995 ne babban taron ƙungiyar kula da harkokin Ilimi, kimiyya da al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya wato UNESCO yayin babban taronta ta nuna girmamawa ga muhimmancin littattafai da marubuta, a wani mataki na ƙarfafa wa jama’a gwiwa musamman matasa game da muhimmancin karatu da kuma girmama waɗanda suka ba da gudunmawa ga harkokin rubuce-rubuce.
Tun lokacin da aka fara ayyana wannan rana, abokan hulɗa suke bikin wannan muhimmiyar rana, lamarin da ya nuna muhimmancin watsa labarai ko amfani da littafi a rayuwar bil-Adama.
Bayanai na nuna cewa, miliyoyin jama’a daga ƙasashe sama da 100 ne suke murnar wannan rana ciki har da daruruwan ƙungiyoyin ƙwararru, da hukumomin gwamnati da ‘yan kasuwa masu zaman kansu. Kamar a jihohin Filato, Kano da Kaduna da Katsina da wasu jihohin ƙasar nan an shirya taruka iri daban-daban. Da suka haɗa da tattakin faɗakar da jama’a muhimmancin karatun littafi, gasar rubutun insha’i na ’yan makaranta da gabatar da laccoci daga manyan marubuta da masu ruwa da tsaki kan harkokin wallafa da talifi.
A iya tsawon wannan lokaci, wannan rana ta littafi da kare ‘yancin haƙƙin mallakar fasaha ta duniya da ake bikinta a ranar 23 ga watan Afrilun kowacce shekara, ta janyo hankulan jama’a daga nahiyoyi da ɓangarorin rayuwa daban-daban, game da muhimmancin littafi da kare ‘yancin mallakar fasaha.
Bincike ya nuna cewa an fara wallafa littafan zube na Hausa ta hanyar shirya gasar rubutun qagaggun labarai domin a samu wadatattun littattafan Hausa domin karantawa.
Gasar Samar Da Ƙagaggun Littattafai Ta Hausa Ta Farko A Duniya ita ce wacce aka gudanar a shekarar 1933, wacce Daraktan Ilimi na Jihar Arewa wanda aka fi sani da Ɗan Hausa, ya ƙaddamar da wani shiri na gudanar da gasar rubutun ƙagaggun labarai don samar da littattafan hira na labarai da rubutun zube.
Waɗanda suka yi nasara aka zaɓi labarun da suka rubuta su biyar ne kamar haka,
Malam Abubakar Imam da littafinsa mai suna ‘Ruwan Bagaja’, sai Malam Bello Kagara da ya rubuta littafin ‘Ganɗoki’,
da Malam Abubakar Tafawa Ɓalewa da littafinsa ‘Shehu Umar’. Akwai kuma Malam Muhammadu Gwarzo mai littafin ‘Idon Matambayi’ da ya zo na huɗu, sai kuma Malam Ahmadu Ingawa da ya samu zuwa na biyar da littafinsa ‘Iliya Ɗan Maiƙarfi’.
Gasar Samar Da Ƙagaggun Littattafai Ta Hausa Ta Biyu A Duniya an gudanar da ita ne a shekarar 1970, wacce kamfanin ɗab’i na Northern Nigerian Publishing Company, wato NNPC, ya shirya domin samar da littattafan adabi na Hausa, kasancewar babu su da yawa a wannan lokacin, kuma Marigayi Dr. Abubakar Imam da Malam Nuhu Bamalli su ne suka jagoranci gudanar da ita.
Waɗanda suka samu nasarar a wancan lokacin su ne, Sulaiman Ibrahim Katsina wanda ya samu nasara a matakin farko, da littafinsa ‘Mallakin Zuciyata’. Sai Hafsat A. Abdulwaheed wacce ta kasance mace ta farko da ta fara rubuta littafin Hausa a arewacin Nijeriya, kuma littafin ta na ‘So Aljannar Duniya’ ya zama na biyu a wannan gasa. Sannan sai littafin ‘Amadi Na Malam Amah’ wanda Malam Magaji Danbatta ya rubuta, ya kasance na uku.
A shekarar 1980 ma Ma’aikatar Al’adun Gargajiya ta Tarayya ta shirya gasar rubutattatun adabi cikin manyan harsunan Nijeriya, inda aka fitar da wasu littattafai bakwai da suka yi fice a harshen Hausa kuma aka buga su. Littattafan kuwa su ne, ‘Turmin Danya’ na Suleiman Ibrahim Katsina, da ‘Tsumangiyar Kan Hanya na Musa Muhammad Bello, sai’ ‘Ƙarshen Alewa Ƙasa’ na Bature Gagare, da kuma Zaɓi Naka na Munir Muhammad Katsina.
Sauran littattafan su ne, ‘Soyayya Ta Fi Kuɗi’ na Hadi Abdullahi Alƙanci, da littafin haɗakar waƙoƙin soyayya na ‘Dausayin Soyayya’ wanda Bello Sa’id ya rubuta, da kuma littafin ‘Wasa Ƙwaƙwalwa’ na Muhammad Yahuza Bello.
Tun daga sannan an riqa samun ƙungiyoyi na gwamnati da masu zaman kansu da ke shirya gasar rubutun adabi da ɗaukar nauyin wallafa littattafai irin su cibiyar Gusau Institute da sauransu. Yayin da wasu suke shirya gasar gajerun labarai, kamar tashar rediyo ta BBC Hausa da suke shirya gasar rubutu ta Hikayata, jaridar Aminiya ta kamfanin Media Trust da sauran ire-irensu.
Sai dai abin tambaya shi ne wanne tasiri waɗannan littattafai suke yi a rayuwar al’umma, wajen canja tunaninsu da qara musu azama a rayuwa? Kuma wacce gudunmawa marubuta ke bayarwa ga cigaban al’umma?
Marubuci kuma lauya mai zaman kansa, Barista Muhammad Lawal Ishaq ya ce, “Ina karanta littafi don ina samun ilimi da ƙwarin gwiwa a kan rayuwa. Da dama daga cikin littattafan da na karanta sun taka rawa wajen saita tunanina akan abubuwan da nake yi na rayuwa.”
Shi ma Alhaji Sani Mu’azu, Makaman Jos ta Arewa, kuma fitaccen ɗan wasan Hausa na Kannywood, cewa ya yi,”Karance-karance da nake yi sun taimaka min wajen ɗaukar darasi da dama a rayuwa da kuma wajen inganta ayyukana na wasan kwaikwayo. Babu shakka nasarori da nake samu a sana’ata na da nasaba da abubuwan da nake karantawa a littattafai.”
Wani malamin makaranta masoyin littattafai, Abdulrazaq Musa Jibril, ya bayyana cewa, sakamakon yawan karance-karance ne ya samu gogewa a ilimin harshen Turanci, da sanin ilimin tarihi da rayuwa.
Babu shakka karatun littattafai na da muhimmanci sosai a rayuwar ɗan adam, musamman wajen inganta tunani da mu’amalar rayuwa ta yau da kullum. Yana nisanta mutum daga shiga ayyukan da ba su kamata ba. Yana kuma ƙara wa mutum ilimi akan wanda yake da shi, irin ilimin da ba lallai ne a karanta shi a littattafan makaranta ba.
Marubuta daban-daban sun fara zama marubuta ne sakamakon karance-karancen littattafan wasu da suke yi, daga nan har su ma suka fara gwada nasu rubutun. Abou Uthaymeen wani marubucin littattafan Hausa ne, ya bayyana min cewa, “Tun ina ƙarami akwai wata yayarmu da take karanta mana littattafai kafin ta yi aure. Wannan ne ya yi tasiri sosai a rayuwata, har na nima na fara yi da kaina.”
Ita ma marubuciya Fadila Lamiɗo ta ce daga karance-karance ta fara samun sha’awar rubutu. “Yawan karance-karancen littattafan Hausa tun ina ƙarama shi ne ya jawo hankalina har na fara sha’awar rubutun labari. Tun lokacin ana rubutawa a takarda, sannan ba a fara rubutu a onlayin ba.”
Da fatan za mu ƙara dagewa da neman ilimi da karatun littattafai don ƙara faɗaɗa tunaninmu da bunƙasa rayuwarmu.
