Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Yayin da Majalisar Dattawa ta 10 ke cika shekara uku da kafa ta a wannan watan Yuni, dokokin gyaran Dokar Zaɓe da kuma Dokokin Gyaran Haraji sun kasance cikin manyan dokokin da suka fi tayar da muhawara da cece-kuce a tsakanin ’yan siyasa, ƙungiyoyin farar hula da al’ummar Nijeriya baki ɗaya.
Rahotanni sun nuna cewa zuwa ranar 29 ga Afrilu, 2026, Majalisar Dattawa ta 10 ta amince da sama da ƙudurori 100 tun bayan rantsar da ita a watan Yunin 2023.
Bayanan da aka samo daga tsarin bibiyar ƙudurorin majalisar sun nuna cewa wasu ƙudurori 38 na jiran karatu na uku, yayin da 453 suka tsallake matakin karatu na biyu.
Sai dai duk da wannan yawan ayyukan majalisa, har yanzu aikin Majalisar Dattawa ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, na ci gaba da janyo ra’ayoyi mabambanta.
Yayin da wasu ke ganin majalisar ta yi fice wajen samar da dokokin da suka shafi gyaran tattalin arziki da inganta harkokin mulki, wasu kuwa na ganin ta kasa taka rawar da ake tsammani daga gare ta wajen kare muradun al’umma da tabbatar da cikakken tsarin dimokuraɗiyya.
Jagoran Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa majalisar ta fuskanci lokuta masu wahala a idon jama’a, musamman lokacin da cece-kucen dakatar da wasu sanatoci da batutuwan ladabtarwa suka mamaye kafafen yaɗa labarai.
A cewarsa, hakan ya sa mutane suka fi mayar da hankali kan rikice-rikice maimakon ayyukan majalisar na samar da dokoki.
Ya ce, duk da haka, majalisar ta samu nasarori masu yawa ta hanyar haɗin gwiwa da ɓangaren zartarwa, musamman wajen ƙoƙarin daidaita tattalin arzikin ƙasa.
Daga cikin dukkan ƙudurorin da aka tattauna a wannan lokaci, ƙudirin gyaran Dokar Zaɓe ya kasance mafi tasiri da kuma mafi yawan cece-kuce.
ƙudirin ya jawo muhawara mai zafi kafin daga bisani Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya masa hannu a watan Fabrairun 2026.
Muhawarar ta fi mayar da hankali ne kan batutuwan aika sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki, tsarin tantance masu kaɗa ƙuri’a na BɓAS, da kuma matsayin dandalin kallon sakamakon zaɓe na IReɓ na INEC.
Masu rajin gyaran tsarin zaɓe da jam’iyyun adawa sun yi imanin cewa dokar wata dama ce ta gyara kura-kuran da suka bayyana a zaɓukan 2023, yayin da wasu ke kallonta a matsayin gwajin sahihancin dimokuraɗiyyar Nijeriya gabanin zaɓen 2027.
Bayan dokar zaɓe, dokokin gyaran haraji su ma sun haifar da muhawara mai faɗi. Bayan watanni ana tattaunawa da yin gyare-gyare, majalisar ta amince da dokokin haraji guda huɗu, waɗanda daga bisani Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu.
Sabbin dokokin na da nufin sauƙaƙa tsarin tattara haraji, daidaita hanyoyin karɓar kuɗaɗen shiga, da kuma rage yawan harajin da ake ɗorawa mutane da kamfanoni.
Sai dai dokokin sun fuskanci adawa daga wasu gwamnonin Arewa, ’yan majalisa da ƙungiyoyi daban-daban, musamman kan yadda za a raba kuɗaɗen shiga da kuma tsarin rabon Harajin ƙarin Kima (ɓAT).
Masu goyon bayan dokokin sun ce za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da ƙara kuɗaɗen shiga daga ɓangarorin da ba man fetur ba, yayin da masu suka ke nuna damuwa kan yiwuwar ƙalubalen aiwatarwa da rashin daidaito tsakanin yankuna.
’Yan sandan jihohi da gyaran Kundin Tsarin Mulki:
Majalisar ta kuma mayar da hankali sosai kan ƙudurorin gyaran Kundin Tsarin Mulki, musamman batutuwan kafa ’yan sandan jihohi, cin gashin kan ƙananan hukumomi, rabon iko tsakanin tarayya da jihohi da kuma gyaran ɓangaren shari’a.
Ko da yake da dama daga cikin ƙudurorin suna ci gaba da bin matakan majalisa, masana na ganin za su iya sauya tsarin tarayyar Nijeriya da yadda ake gudanar da mulki a nan gaba.
Har ila yau, majalisar ta amince da wasu ƙudurorin kafa hukumomin bunƙasa yankuna daban-daban, duk da cewa masu suka suna nuna damuwa kan yiwuwar maimaita ayyukan hukumomi da ƙarin nauyin kashe kuɗaɗen gwamnati.
Shugaban ƙungiyar Masana Kimiyyar Siyasa ta Nijeriya (NPSA), Farfesa Hassan Saliu, ya ce abin da ya fi muhimmanci ba wai kusancin da ke tsakanin ɓangaren zartarwa da majalisa ba ne, illa sakamakon da wannan haɗin gwiwa ke haifarwa ga talakawan Nijeriya.
Ya bayyana cewa tambayar da ya kamata a yi ita ce ko dokoki da manufofin da ake samarwa suna inganta rayuwar jama’a.
Game da dokar zaɓe kuwa, Farfesa Saliu ya ce duk jam’iyyar da ke da rinjaye a majalisa za ta yi ƙoƙarin tsara dokoki da za su amfaneta ta fuskar siyasa, amma ya yi gargaɗin cewa dole ne a kare sahihancin zaɓe da amincewar jama’a da tsarin dimokuraɗiyya.
Ya kuma yi kira ga INEC da ta kasance cikin shiri wajen tabbatar da gaskiya da adalci a dukkan matakan zaɓen 2027.
