Janar Musa zai kutsa daji da ’yan soshiyal midiya?

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Dama ba baƙon abu ba ne tafiya da kwararrun ’yan jarida ko kuma wakilan kafafen labaru na ɓangaren tsaro, sassan da a ke gumurzu don su ganewa idonsu yadda a ke fafatawa su kuma ɗauko labaru da samun hirarraki na musamman. Hakan ya kan sa su iya samun sauyin tunani daga yadda su ke hango ayyukan dakaru daga nesa ko taruka cikin dakuna masu na’urorin sanyaya ɗaki. Babban ministan tsaro Janar Christopher Musa ya bayyana aniyar tafiya da wasu daga masu tasiri a yanar gizo zuwa fagen daga don irin wannan manufa.

Janar Musa ya kafa hujjar yunkurin tafiya da wasu manyan ‘yan yanar gizo zuwa fagen yaƙi ne don yadda wasu ke shirin gudanar da zanga-zanga don matsawa gwamnati lamba ta magance matsalar tsaro. Shin yin zanga-zanga na iya kawo tsaron ko sauya wani abu daga halin da a ke ciki? Amsar wannan tambaya ta na cikin niyyar Janar Musa ta tafiya da ‘yan yanar gizon nan, don ba mamaki in sun ga zahiri yadda a ke ɗauki ba daɗi da miyagu, su ajiye tunanin zanga-zanga.

Yadda wasu ‘yan yanar gizo ke nuna gazawar hukumomi da nada kansu zama ƙwararru kan tsaro har ma da ganin in an ba su dama za su iya ƙunduma dazuka su yi yakin da kansu, ya sa irin hakan zai iya taimakawa wasu masu hankali a ciki su gane ba kwantawa barci dakarun ke yi a bakin dazuka ba. Kai wasu ma har shawara ko zugawa su ke yi cewa mutane su dau makamai a yi ta ta kare! Kuma duk rashin gane illar fararen hula su zama da makamai a hannunsu ne ya jawo haka. Wallahi in an bar mutane su ka mallaki makamai duk wannan asarar rayuka da a ke gani na kowane ɓangare nafila ne.

Idan a ka bar ƙasa a hannun ‘yan banga kamar yadda sassan Libya su ke, shikenan an koma ƙara-zube kenan mai ƙarfi ya doke marar ƙarfi. Hatta masu wuƙaƙe da wasu gwamnoni su ka ɗauka ai sun kashe waɗanda ba su yi mu su laifin komai ba a Katsina da Zamfara. Ba zai yiwu a ɗau wasu katti kawai marar sa kwarewa a rayuwar duniya su zama wai za su kawo tsaro ba. Dole jami’in tsaro ya samu horo na musamman don wannan aiki na tsaron rayuka da dukiya ba kawai wani mai hura ƙaho ko gagarau a kauye ba mai ganin rai tamkar ƙarar tabar da ya ke shekar da hayaƙinta a iska ba.

A watannin baya, ba wasu ma sun ɗauka da zarar an sauya ministan tsaro Alhaji Badaru shikenan za a samu tsaro ba, tun yaushe Badaru ya bar kujerar? Wannan ƙalubale fa ba da fushi ko makirci da molon ka za a magance shi ba. Ya zama wajibi a ƙara samun fahimta tsakanin hukuma da jama’a kan gwagwarmayar nan. Baƙaƙen maganganu ba za su taɓa gyara illar ba har abada.

Duk masu amfani da fasahar AI wajen ɗinka kayan soja na neman maida lamarin abun barkwanci wanda ba haka ya kamata a yi ba. Ai rigar FALMARA ta gidan jarida a ke bayarwa mai rubutu manya-manya PRESS idan za a yi wannan fita.

Ina marawa Janar Christopher Musa baya wajen wannan niyya don za ta iya wanke idon na bayan fage gwanayen kokawa su fahimci yakin nan ya ƙunshi na sunkuru da kuma yanayin ta’addanci da ke da wuyar gamawa ta tunanin kwab daya. Kazalika ina kira ga hukumomi su cafke duk mai ingiza cigaba da fitinar nan don cimma burin kyasta ashana ga Arewa da zummar tallafawa burin ‘yan aware da masu son kafa tungar ƙabilu a musamman Arewa ta tsakiya.

Mu dawo kan batun shirin tafiya da masu labarun gizo fagen daga da ministan tsaro ya ayyana a wani jawabi da ya gabatar.

Kamar yadda na fada kalaman babban ministan tsaro Janar Christopher Musa na tunanin yin shiri tafiya da wasu ‘yan soshial midiya fagen yaƙi sun biyo bayan niyyar da wasu ‘yan labarun yanar gizo su ka dauka ta yin zanga-zanga kan taɓarɓarewar tsaro. Na yi ƙoƙarin fassara kalaman da Hausa kamar haka:

“Na gani a ‘yan kwanakin nan wasu manyan masu labarun yanar gizo nuna nufin yin zanga-zanga. Ba wanda ya dakatar da wani daga zanga-zanga amma ya kamata mu yi la’akari da abubuwan da ka iya biyowa baya da ba a yi nufi ba inda wasu za su karkatar da hakan kuma ya sanya a iya raunatawa ko kashe mutane. Mu na ƙoƙarin samar da dama ga wasu daga cikin waɗannan kwararru na labaru mu shigar da su cikin dakaraunmu lokacin da za su tafi aiki Arewa maso gabar, Arewa maso yamma ko Arewa ta tsakiya saboda su ji kuma su ganewa idonsu ƙalubalen da dakaru ke shiga. Watakila haka zai sa su fahimci yadda lamuran ke gudana.”

A yanar gizo mun sha ba da labarin masu neman murɗe yanayin taɓarɓarewar tsaro zuwa ƙabilanci da ma neman aibata wasu magabata da su ka bar duniya tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka.

In ka deɓe logar fitowa da suna da hoton karya da makiran bayan fage su ka tsarawa ‘yan yaudarar Hausa zalla, masu tsara mu su kalamai THINK TANK sun fara da babban kuskuren cewa “ƙabila ta fi addini” wanda hakan neman ridda ne daga Musulunci. Kazalika ware wasu wai limamai ko malaman wata ƙabila kaza da kaza sam ba zai samu karbuwa ba a tsakanin musulmi Hausawa sam, don yau in da Musulmin Arewa kakaf za su taru a wani fili ko a babban masallacin Abuja, za su bi Iman Sheikh Iliyasu Tochwukwu ba tare da tunanin ƙabilarsa ba don musulunci ya yi watsi da ƙabilanci a matsayin ɗabi’a mai kazanta ta jahiliyya.

Na taɓa kawo ƙalubale ga ‘yan yaudarar Hausa zalla da ke cewa su Musulmi ne su yi Kalmar Shahada to hatta wani madugunsu bai iya Kalmar shahada ba balle wani ɗan figegge sabon yankan rake a gonar shisha.

Akwai illar ɗaukar marar sa ilimi a irin wannan gagarumar kwangilar rusa Arewa don wasu kullum kalmomin da a ka lakkana mu su, su ke maimaitawa kuma ga misalai a kasa. Duk da mun san sun ɗauka in sun yi ta maimaita kalmomin, karshe duk munin karya za ta juye zuwa abin yarda. A kan yarda da abin da bai ci karo da koyarwar addini da al’adun jama’a musamman mai bin addinin tauhidi irin Arewa ba. Yammawa masu jan kunne ma sun jarraba sauya akalar al’ummar Arewa amma haka su ka koma da hayaƙin tabarsu!.

A baya-bayan nan ba abin da ya ɗau hankalin masu sharhin sa-kai da kwarewa ko akasin haka na yanar gizo irin babban akasin da a ka samu na rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar a hannun ‘yan ta’adda.

Hausawa na cewa KOWANE MAI RAI MAMACI NE da ma’anar dukkan talikkai za su koma ga Allah watarana inda sanadin komawar kan zama ta hanyoyi daban-daban. Manjo Janar Rabe Abubakar na daga fitattun mutane da wannan ƙaddara ta aukawa bayan Allah ya ba shi dama ya yi aikin hidima ga ƙasa a rundunar sojan ƙasan Nijeriya har ya yi ritaya. A baya ma na ke misali da kisan giilla ga Manjo Janar Muhammad Idris Alkali a Dura-Du Jos wanda shi ma ya yi aikin soja har ya yi ritaya lafiya inda kaddarar ta auku ta hannun miyagun iri marar sa son zaman Arewa da Nijeriya lafiya. A ranar 9 ga Afrilu ma a ka rasa Burgediya Janar Oseni Omoh Braimah da dakaru 17 a Benisheikh jihar Borno.

Mu na fatan kamar yadda dakaru su ka yi nasarar tarwatsa tungar ‘yan ESN su ka gano inda a ka bunne gawar Warrant Office Linus Musa Audu da Lance Corporal Gloria Mathew a jihar Imo, za su wargaza tungar dukkan masu barazana ga zaman lafiya.

Wannan fitina ta zama ruwan dare kuma ta kan iya faɗawa kan duk wanda ƙaddarar ta samu ba babba ba yaro ba mai kayan Sarki ba mai farar hula. A Arewa tun 2009 a ke cikin wannan yanayi duk da ya na canjawa kamar hawainiya daga Arewa maso gabar zuwa Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya. Don haka wasu yara ‘yan goma sha zuwa ashirin kan iya ɗaukar dama haka Arewa ta ke don ba su tashi a zamanin da mutum zai taso daga Ilori zuwa Maiduguri lafiya ƙalau ko daga Illela zuwa Tsaunukan Mambilla ba wata fargaba sai ta duhun dare ko ‘yan ramukan kan titi ba ko jami’an duba hanya na su Ummarun Yola a waƙar Dokta Mamman Shata ba “idan ka ga idon na kunya ne rabe can jikin icce iza yara Ummarun Yola..”

KAMMALAWA

Jama’a a cigaba da haɗa kai da jami’an tsaro don amintar da ƙasarmu daga miyagun iri. Jami’an tsaro su kaɗai ba za su iya gano komai ba kuma ko da ta amfani da fasahar zamani da irin jiragen nan marar sa matuƙa. Haƙiƙa mai ɗaki shi ya fi sanin inda ya ke yi ma sa yoyo musamman ga irin wannan fitina ta ‘yan sari-ka-noke. Duk take-taken da ba a gane ba a san dabarun da za a wargaza gadar zaren miyagun iri.

By ukarofi

Leave a Reply