Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Tsohon babban sakatare kuma raya karkaran Katsina, Alhaji Abu Ɗanmalam Karofi ya rasu bayan yayi fama da doguwar rashin lafiya a Katsina.
Ɗanmalam Karofi wanda aka fi sani da ADK shi ke kula da ƙananan hukumomin jihar a lokacin Marigayi Umaru Musa Yar’adua na gwamnan jihar.
Marigayi ADK za a riƙa tunawa da shi wajen jajircewa na ganin shugabannin ƙananan hukumomi dole su gaskiya da riƙon amana wajen tafiyar da mulkin ƙananan hukumomin jihar.
Haka kuma an bayyana Karofi a matsayin mai gaskiya da jajircewa wajen ganin shugabannin ƙananan hukumomi sun sarrafa kason kuɗaɗen su yadda ya dace.
An yi jana’izar sa a mahaifarsa da ke Rayuka a cikin garin Katsina.
