‘Yan sanda sun kama wani matashi bisa zargin kashe mahaifinsa a Katsina

Spread the love

Wani matashi ɗan shekaru 27 ya yi sanadiyyar mutuwar mahaifinsa mai shekaru 80 a ƙauyen Mundadu da ke ƙaramar hukumar Bindawa ta Jihar Katsina.

Matashin mai suna Sada Tambai, ya shiga hannun ’yan sanda bisa zargin aikata abin da ya yi sanadin mutuwar mahaifinsa, Adamu Tambai, wanda ya kasance tsohon dagacin unguwar Mundadu.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar,lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Satumba, 2026, bayan da aka samu rahoton cewa Adamu Tambai ya kasance kwance ba ya motsi a gaban gidansa.

‘Yan sanda sun garzaya da shi zuwa asibiti domin samun agajin gaggawa, amma likita ya tabbatar da rasuwarsa.

Binciken farko da ’yan sanda suka gudanar ya kai ga kama ɗan marigayin.

Rundunar ta ce yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya buga wa mahaifinsa sanda a kai, abin da ya haifar da raunin da daga bisani ya yi sanadin mutuwarsa.

Lamarin ya jefa iyalai da al’ummar yankin cikin alhini da jimami, musamman ganin cewa wanda ake zargin ɗan marigayin ne.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, ya bayar da umarnin tura lamarin zuwa sashin bincike na mayan laifuka a rundunar domin gudanar da cikakken bincike.

CP Fage ya yi ta’aziya ga iyalai da al’ummar ƙaramar hukumar Bindawa kan wannan mummunar lamari ya kuma tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda za su yi cikakken bincike kuma da zarar sun kammala za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu.

Masana harkokin yau da kullum na masu ra’ayin cewa yawatar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa ya ƙara jefa al’umma cikin irin wannan yanayi.

Dole sai hukumomin tsaron,Iyayen ƙasa da malaman addini sun haɗa ƙarfi da karfe wajan shawo kan matsalar shaye shaye a Jihar Katsina.

By ukarofi

Leave a Reply