Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙungiyar marubuta labarin wasanni ta ƙasa (SWAN),reshen Jihar Katsina,ta taya babban uban ƙungiyar,Alhaji Usman Isyaku,murnar samun lambar yabo ta gwarzon mai ba gwamna shawara da ya fi ƙwazo a jihar.
Alhaji Usman Isyaku,wanda shi ne mai ba gwamnan Jihar Katsina shawara kan farfaɗo da aikin gwamnatin ya samu wannan lambar yabo ne bisa gudunmawarsa wajen ci gaba da inganta harkokin ma’aikatan gwamnati da kuma kawo sauye sauye a tsarin aikin gwamnatin jihar.
A cikin sakon taya murna,shugaban ƙungiyar ta reshen Jihar Katsina, Malam Nasiru Sani Gide, ya bayyana wannan karramawa a matsayin shaida da ke nuna irin jajircewa, kokari da gudunmawar Alhaji Usman Isyaku wajen inganta ayyukan gwamnati da samar da ingantaccen hidima ga al’ummar Jihar Katsina.
Ya bayyana cewa Katsina SWAN na alfahari da wannan nasara yana mai yaƙinin lambar yabo za ta ƙara ƙarfafa gwiwar wanda aka karrama wajen ci gaba da kokarinsa na ganin an samu ingantaccen tsarin aikin gwamnati da ci gaba a jihar.
SWAN ta yaba da yadda uban ƙungiyar ke taimakawa da shawarwari na ƙarfafa gwiwa ga ƙungiyar marubuta wasanni a jihar.
Ƙungiyar ta kuma yi wa SA Isyaku fatan alheri da samun nasarori da ɗaukaka da tsawon rayuwa mai amfani.
