(Me ya sa foundation ya zama abin so ga mata?)
Daga AISHA ASAS
Ba za a iya fahimtar muhimmancin foundation a duniyar kwalliya ba tare da duba yadda mata suke kallon kyawun fuska da kuma irin sauyin da suke son samu bayan sun kammala kwalliya ba.
Ga mace mai tabo a fuska, foundation na iya taimaka mata ta rage bayyanar waɗannan tabo na ɗan lokaci. Ga wadda launin fuskarta bai yi daidai ba, zai iya taimaka mata wajen daidaita kamannin fatar. Ga wadda take son kwalliyarta ta kasance da santsi da tsari, foundation na iya zama muhimmin ɓangare na cimma wannan buri.
Haka kuma, a wuraren da ake ɗaukar hotuna ko yin bidiyo, foundation na taimaka wa kwalliya ta fito da kyau, musamman idan an zaɓi wanda ya dace da launin fata, aka shafa shi yadda ya kamata, sannan aka haɗa shi da sauran kayan kwalliya cikin tsari.
Wannan shi ne dalilin da ya sa ake samun nau’o’i masu yawa a kasuwa, wasu masu sauƙin rufewa, wasu kuma masu ƙarfi wajen ɓoye alamomin fata. Akwai masu ba da kamannin fuska mai haske, akwai kuma waɗanda ke rage yawan sheƙi ga masu fata mai maiko.
Sai dai, a nan ne zaɓi ya zama wajibi. Domin foundation da ya yi wa wata mace kyau, ya kuma zauna lafiya a fatarta, ba lallai ne ya dace da wata mace ba. Abin da ya fi muhimmanci ba wai shaharar samfurin ko farashinsa ba ne, sai yadda ya dace da irin fatar mai amfani da shi da kuma yadda take kula da fuskarta kafin da bayan shafa shi.
Shin foundation na iya hana fata numfashi?
Wannan na daga cikin tambayoyin da ake yawan yi game da kayan kwalliya. Wasu na ganin cewa idan mace ta riƙa shafa foundation, fatar fuskarta za ta kasa numfashi, daga ƙarshe ta lalace.
Amma binciken da kafar yaɗa labarai ta Channel NewsAsia ta wallafa a shafinta na salon rayuwa da kwalliya a ranar 18 ga Mayun 2021, wanda aka sabunta a ranar 31 ga Agustan 2022, ya yi ƙoƙarin bambance gaskiyar kimiyya da wannan fahimta.
A cikin rahoton, Dr Eileen Tan, ƙwararriyar likitar fatar jiki a Eileen Tan Skin Clinic & Associates da ke Mount Elizabeth Novena Hospital, Singapore, ta bayyana cewa maganar cewa fata tana buƙatar numfashi kamar yadda huhu yake numfashi ba gaskiya ba ce a kimiyyance.
A cewarta, fatar jiki ba ta ɗaukar iskar oɗygen daga sararin da ke kewaye da ita kamar yadda huhu yake yi. ƙwayoyin fatar da ke saman jiki sun bambanta da waɗanda ke zurfinta, kuma sassan da ke buƙatar iskar oɗygen da abubuwan gina jiki suna samun su ta hanyar jini.
Saboda haka, matsalar da ya kamata a fi mayar da hankali a kanta ba wai ko foundation ya hana fata numfashi ba ne, sai dai ko samfurin yana toshe ramukan fata, ko yana saka kuraje, ko kuma yana jawo wani yanayi da zai cutar da fatar mai amfani da shi.
Dr Tan ta kuma bayyana cewa foundation na iya taimakawa wajen toshe ramukan fata, amma ba shi kaɗai ne ke iya haifar da wannan matsala ba. Wasu kayayyakin kula da fata da ma wasu man kariya daga rana ma na iya haifar da irin wannan matsala, gwargwadon sinadaransu da irin fatar da aka shafa musu.
Wannan bayani yana nuna cewa ba daidai ba ne a ce duk foundation na lalata fata. Abin da ya fi muhimmanci shi ne nau’in samfurin da aka zaɓa, yadda ya dace da fata, da kuma ko ana cire shi yadda ya kamata bayan an gama amfani da shi.
