
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, da Ma’aikatar Harkokin Hajji da Umara ta Saudiyya, sun ƙulla yarjejeniyar MoU domin harkokin Hajjin 2027 da inganta lamuransa.
An ƙulla yarjejeniyar ne a ranar Talata, 10 ga Nuwamba, 2026 a Jiddah, wadda Shugaban NAHCON, Ambasada Isma’il Abba Yusuf ya wakilci Nijeriya yayin ƙullawa, inda Mataimakin Ministan Hajji da Umarar Saudiyya, Dakta Abdulfattah bin Sulaiman Mashat ya wakilci Saudiyya, kamar yadda sanarwar da Kakakin NAHCON, Shafi’i Sani Mohammed ya fitar ta bayyana.
A cewarsa, wannan yarjejeniya ta samar da tsarin shirya shigar Nijeriya aikin hajji, ciki har da adadin alhazan da za a ware mata, biyayya ga dokokin Saudiyya, kiyaye wa’adin ayyuka da haɗin kai a muhimman al’amura kamar masauki, sufuri da kiwon lafiya. Haka kuma, ta samar da tsarin haɗin-gwiwa tsakanin ƙasashen biyu domin warware ƙalubalen kayayyaki, kula da ingancin hidima da bai wa walwalar alhazai kariya.
Da yake jawabi a taron, Ambasada Yusuf, ya yaba wa gwamnatin Saudiyya da ma’aikatar hajji da umarar kan cigaba da faɗaɗa lamuran walwalar alhazai, muhimman cigaba da aka samu wajen tsare-tsaren hajji da ɗorewar haɗin-gwiwa da Nijeriya. Ya kuma jaddada ƙoƙarin NAHCON na haɗewa da waɗannan nasarori ta bunƙasa haɗin-gwiwa da inganta hidimar hajji ga ‘yan Nijeriya.
Shi ma a tsokancinsa, Dakta Mashat ya ce, Ƙasar Mai Tsarki ta yi nasarar samun kaso 93 na gamsar da alhazai yayin harkokin hajji, yana mai yaba wa Nijeriya bisa gudummawarta tare da kira ga NAHCON da ta yi ƙoƙarin ɗorewa kan haka.
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da jakadan Nijeriya ga Saudiyya, Ambasada Yakubu Gambo; da mambobin Majalisar Dokokin Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Hon. Jafar Mohammed, wanda shi ne shugaban kwamitin Hajji tare da wasu manyan jami’an gwamnati. A ƙarshe, Kakakin ya ce NAHCON za ta haɗa hannu da hukumomin alhazan jihohi da sauran masu ruwa da tsaki wajen aiwatar da shirye-shiryen hajjin bisa inganci.



