FUDMA ta karrama shahararren mawaƙi Ala a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Sashen nazarin harshen Hausa na Jami’ar Tarayya ta FUDMA da ke Dutsinma a jihar Katsina ta shirya taron ƙasa da ƙasa na farko kan nazari da bitar ayyukan adabi na shahararren marubuci kuma mawaƙi, Alhaji Aminu Ladan Abubakar, wanda aka fi sani da Alan Waƙa.

Taron wanda aka gudanar a ɗakin taro na Hillside da ke cikin garin Katsina na da nufin nazari da tattauna gudummawar da Ala ya bayar wajen bunƙasa harshen Hausa, adabi da al’adu, tare da duba tasirin ayyukansa ga al’umma da kuma ci gaban harshen Hausa a wannan zamani.

Haka kuma, taron ya haɗa Sarakuna, masana, malamai, masu bincike, marubuta da ɗalibai daga sassa daban-daban na kasar domin gabatar da ƙasidu da tattaunawa kan fannoni daban-daban na ayyukan adabin Ala.

A jawabinsa ,shugaban jami’ar FUDMA Farfesa MK Othman ya bayar da takaitaccen tarihin jami’ar da kuma irin nasarorin da aka samu zuwa yanzu.

Haka zalika shugaban taron Ambassador Ahmad Rufa’i Abubakar Sardaunan Katsina ya bayyana muhimmanci da wakokin Ala suke bayarwa ga harshen Hausa.

Ya ƙara da cewa wannan taro zai taimaka wajen adana tarihi da bunƙasa bincike a kan adabin Hausa, tare da ƙarfafa wa matasa gwiwar nazarin ayyukan marubuta da mawaƙan Hausa.

Daga cikin mutanen da suka yi jawaban fatan alheri sun haɗa da Sarkin masarautar ,Kano Alhaji Aminu Ado inda daga bisani Alhaji Ibrahim Ida da sauran baƙi suka gabatar da lakcoci akan adabi da harshen Hausa.

By ukarofi

Leave a Reply