
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jami’an tsaro a Jihar Kogi, sun ce sun fara bincike sakamakon tserewar wasu fursunoni guda biyu daga gidan yarin Okene domin kamo su. Al’amarin ya auku ne a ranar Lahadi, 8 ga Nuwamba, 2026 a cewar wani rahoton ‘yan sanda na Ofishin Okene.
Rahoton, wanda ba a bayyana mawallafinsa ba, ya bayyana cewa waɗanda suka tseren sune Samson David da aka tsare kan sata da kuma Salvation Moro da aka tsere kan fashi da makami.
A cewar rahoton, jami’in da ke kula da kurkukun ya sanar da ‘yan sanda batun ta wayar tarho da misali ƙarfe 10:30 na safiyar ranar Lahadi. An ce fursunoni biyun sun tsere ne ta katangar baya ta gidan gyaran yarin.
Sannan, an wallafa hotunansu a jikin takardar rahoton ‘yan sandan domin sauƙin gano su da ɗaukar matakan da suka dace akansu. Saidai ba a bayyana ainihin yadda al’amarin tserewar ta kasance ba.
