Daga SANI GAZAS CHINADE Damaturu
Rikicin shugabanci da ya dabaibaye reshen jihar Yobe na majalisar ba da shawara kan jam’iyyun siyasa ta Najeriya (IPAC) ya ƙara ta’azzara, inda shugaban jihar, Umar Adamu Jajere, da babban sakatare, Mustapha Gado, suka yi watsi da yunƙurin tsige su da wasu mambobin IPAC suka yi.
A cikin wata sanarwar da shugaban da sakataren suka bayar ga manema labarai a Damaturu sun bayyana matakin a matsayin wanda bai da tushe, inda suka dage cewa su ne shugabannin da aka amince da su na reshen IPAC na jihar har zuwa yau.
Wannan lamari ya haifar da sabbin tambayoyi kan shugabanci da tafiyar da harkokin cikin gida na wannan majalisar bada shawara ta haɗakar jam”iyyun siyasa IPAC a jihar, musamman yayin da harkokin siyasa ke ƙara samun ƙwarin gwiwa gabanin babban zaɓen 2027 da ke tafe.
A cikin sanarwar shugaba da sakataren sun nuna rashin amincewa da kuma watsi da wasu tsirarun mambobi suka rattaɓa hannu a kai yadda shugaban da sakataren, majalisar suka ce tsige wa da aka yi ya saɓa wa tanade-tanade da dama na kundin tsarin mulki na IPAC (2019) kuma ba za a iya amincewa da shi ko kaɗan ba.
A cewar sanarwar, taron bai samu kashi 50 na mambobin majalisar zartaswa ta jiha ko majalisar jiha ba, kamar yadda sashi na 8(ii) da 8(iv) na kundin suka tanada.
Don haka majalisar ta kuma yi zargin cewa mutanen da shugabannin jam’iyyunsu na jiha ba su ba da sunayensu a rubuce ba ne suka shiga kuma suka kaɗa ƙuri’a a taron, wanda ya saɓa wa sashi na 4.2(a) da 15.
Majalisar ta ƙara da cewa taron ba a kira shi yadda ya kamata ba, inda suka yi ikirarin cewa babu buƙatar a rubuce da kashi biyu bisa uku na mambobin da suka sanya hannu kuma ba a ba shugaban sanarwar kwanaki bakwai da ake buƙata kamar yadda sashi na 8(vii) ya tanada ba.
Dangane da tsarin ladabtarwa, jami’an sun ce babu wani koke da aka miƙa wa kwamitin ladabtarwa ko kwamitin sulhu na jam’iyyun siyasa (PPADR), kuma ba a gudanar da wani bincike ba kafin tsige su da aka yi ikirarin aiwatar wa.
Don haka majalisar ta yi gargaɗin cewa duk wanda ke nuna kansa a matsayin jami’in IPAC a jihar Yobe bisa tsige wa da aka yi, yana yin hakan ne ba tare da ikon doka ba.
Ta kuma yi barazanar ɗaukar matakin ladabtarwa, har da dakatarwa, ga mambobin da suka shiga cikin wannan aiki, inda ta zarge su da saɓa wa kundin tsarin mulki na majalisar.
IPAC ta buƙaci gwamnatin Jihar Yobe, hukumar zaɓe ta Jiha (YOSIEC), hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da sauran masu ruwa da tsaki a fannin siyasa da su amince da Jajere da Gado a matsayin halastattun shugabannin jihar kaɗai.
Ta ƙara da cewa an sanar da sakatariyar ƙasa ta majalisar dangane da lamarin kamar yadda sashi na 4.3 na kundin ya tanada.
Ƙungiyar ta sanar da tsigewa da aka yi har yanzu ba ta mayar da martani kan sanarwar ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.
