
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci-gaban Sararin Samaniyar Nijeriya, Festus Keyamo, ya bayyana cewa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) za ta shiga zaɓukan 2027, amma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da wasu ‘yan takara da tsagin jagorancin jam’iyyar na su tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark ba lallai su wakilce ta ba.
Keyamo ya kuma yi watsi da iƙirarin yaɗa cewa hukuncin Babbar Kotun Tarayya na kwanan nan kan shugabanci ka iya hana ADC shiga zaɓen, yana mai cewa bai dace a riƙa fassara hukuncin a matsayin soke jam’iyyar ba. Ministan ya wallafa wannan bayani ne a shafinsa na X a ranar Lahadi, inda ya ce akwai buƙatar a bambance hukuncin kotu da cancantar ‘yan takarar da tsagin su Mark ta fitar.
Ya kuma ƙalubalanci dalilin da ya sa ‘yan Nijeriya da suka samu tikiti ta ainihin masu jam’iyyar ADC suka rasa damar shiga takara a zaɓukan 2027, yana mai cewa dukkan ɓangarorin suna da ‘yanci daidai a dokance ba tare da wani ɓangare ya ɗara wani ba.
Kalaman ministan na zuwa ne yayin rikicin da ya mamaye jam’iyyar adawar bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ya soke jagorancin kwamitin riƙo na su Mark. A ranar Juma’a ne dai Ministan Sufurin ya ce sama ba za ta rikito ta haɗe da ƙasa ba don ba a sanya Atiku Abubakar a cikin sahun ‘yan takarar Shugaban ƙasa ba a zaɓen 2027 da ke tafe.
