
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun halaka mutum guda 12 ‘yan gida ɗaya a ƙauyen Gidan Taba da ke Gundumar Dosara Birnin Ƙaya ta Ƙaramar Hukumar Maradun a jihar Zamfara, bayan sun cinna wa wani gida wuta da a nan mutanen suka laɓe a lokacin da ‘yan bindigar suka kaiwa yankin nasu farmaki.
Rahotanni sun ce, maharan sun kuma sace wasu mutane da ba kai ga sanin adadinsu ba yayin harin, wanda ya auku a safiyar ranar Lahadi, lamarin da ya jefa al’umma cikin jimami.
Wani mazauni ‘yankin da ya nemi a sakaye sunansa, ya shaida wa ‘yan jarida cewa mamatan ‘yan gidan wani Mallam Muhammadu Sani ne, wanda ya ɓoye matarsa da qasu ‘yan gidan nasa a wani ɗaki da nufin ba su kariya daga harin ‘yan bindigar.
A cewarsa, a lokacin da maharan suka gano haka cewa iyalan sun rufe kansu a cikin wani ɗaki, sai suka nemi su buɗe, su kuma suka ƙi bada haɗin kai, lamarin da ya maharan suka banka wa gidan wuta, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar baki ɗaya mutane 12 da ke ciki. Baya ga waɗanda aka halaka, ‘yan bindigar sun kuma sace wasu da dama yayin harin duk da cewa ba a iya gano adadinsu ba yayin haɗa wannan rahoto.
Tuni dai aka yi wa gawarwakin mamatan 13 jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada yayin jimamin rashinsu. Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, gwamnatin Zamfara ko ‘yan sanda ba su fitar da wani bayani a kai ba.
