
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta jaddada aniyarta ta tabbatar da gudanar da zaɓukan 2027 bisa gaskiya da adalci, tana mai tabbatar wa ‘yan ƙasa da ‘yan waje cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta cigaba da ƙarfafa cibiyoyin dimukraɗiyya da kare martabar lamuran zaɓukan ƙasar.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris ne ya bayar da wannan tabbaci yayin hira da kafar TRT Word ta Turkiyya, a fagen tattaunawa ta ‘TRT World Forum 2026’, da ake gudanarwa a Istanbul, babban birnin ƙasar. An fara taron ne a ranar Juma’a, 6 ga Nuwamba, 2026 mai taken: A World Without a Centre: ‘Who Leads When the Rules Run Out?’
Ya ce, gwamnatin Tinubu tana girmama muhimmancin zaɓuka na gaskiya ga shugabancin dimukraɗiyya kuma za ta samar da dukkan tallafin da ake buƙata ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), yayin girmama ‘yancinta na doka. Ya bayyana cewa, gwamnatin tana ƙoƙarin samar da yanayin da zai bai wa INEC damar sauke nauye-nauyen da suka rataya akanta ba tare da tsoma mata baki ba da kuma tabbatar da girmama zaɓin ‘yan Nijeriya a lokacin zaɓukan.
A cewarsa, bai wa INEC tallafi ba ya nufin tauye ‘yancinta na cin gashin kai, saidai ana haka ne bisa la’akari da nauyin da ya rataya a wuyanta na shiryawa da gudanar da zaɓuka a Nijeriya. Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da shirye-shiryen zaɓukan 2027, inda masu ruwa da tsaki suka faɗaɗa shiri ga hanyoyin gudanar da zaɓukan.
Da yake tsokaci kan halin tsaro a Nijeriya musamman bisa la’akari da tasirinsa a zaɓen da ke tafe, ministan ya ce Gwamnatin Tarayya tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta daƙile ƙalubalen tsaro a sassan ƙasar, yana mai cewa fannin tsaro ɗaya ne ɗaga cikin muhimman ababen da gwamnatin take fifitawa musamman ganin yadda Shugaba Tinubu yake ƙarfafa wa lamuran hukumomin tsaron ƙasar ta hanyar ɗibar sabbin jami’ai da siyo makamai.
