
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
‘Yan matan Nijeriya na tawagar ƙwallon ƙafar Flamingos na mata ‘yan ƙasa da shekara 17, sun dawo gida Nijeriya bayan nasarar lashe Kofin Duniya na 2026 a Moroko.
Matasan taurarin sun isa filin jiragen saman na Nnamdi Azikiwe ne a safiyar yau Litinin, 9 Nuwamba, 2026, inda suka kawo kofin gida bayan doke Japan a wasan ƙarshe da ci 2 da 1 a ranar Asabar a Birnin Rabat. Wannan ya kawo ƙarshen kakar mai tarihi ganin cewa Nijeriya ce ƙasa ta farko a Nahiyar Afirka da ta taɓa lashe kofin na FIFA U-17 Women’s World Cup.
Sannan Flamingos ce tawagar Afirka ta farko da ta lashe kofin da FIFA ta shirya a ɓangaren maza da mata ‘yan ƙasa da shekara 17. Duk da cewa Nijeriya ta fuskanci rashin nasara da ci 2 da 1 a wasan farko da ta yi da Poland, hakan bai sa ta yi ƙasa-a-gwiwa ba wajen cimma burinta na lashe kofin.
Wannan na wakiltar gagarumar nasara ga Nijeriya duba da cewa ba ta taɓa kaiwa matakin wasan ƙarshe ba a gasar FIFA. Saidai a baya a shekarar 2022 Nijeriya ta kai matakin wasan dab da na ƙarshe a 2022, inda ta ƙare a matsayi na uku a gasar da aka yi a Indiya.
Kazalika, hakan ƙarin nasara ce ga waɗanda ɓangaren maza suka samu na ‘yan ƙasa da shekara 17 har sau biyar, wato a shekarun 1985, 1993, 2007, 2013 da 2015. Lashe na matan a yanzu ya nuna cewa, Nijeriya ta bi sahun Faransa a matsayin ƙasashen da suka lashe gasar ɓangaren mazan da na mata ‘yan ƙasa da shekara 17.
