Shugaban APC da aka sace a Kano ya shaƙi iskar ‘yanci bayan kwana 68

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta ce ta yi nasarar ceto Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Rogo, Abdullahi Alasan Beli, wanda aka sani da Abdullahi Fanka, bayan shafe tsawon kwanaki 68 a hannun masu garkuwa da mutane.

Kwamishinan ‘yan sandan, CP Ibrahim Bakori ne ya sanar da haka yayin bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar ba’asi a Gidan Gwamnatin Kano, kamar yadda kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, 2026.

An yi garkuwa da Beli ne a gidansa da ke ƙauyen Beli a Ƙaramar Hukumar Rogo a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai wani farmaki a yankin, inda suka tafi da shi wurare daban-daban a jihar Kano da jihohin maƙota. Da yake jawabi bayan shaƙar iskar ‘yancin, Shugaban na APCn, ya bayyana cewa masu garkuwar sun garzaya da shi ne ta yankunan Ɗanja a Katsina da Ikara da Giwa a Kaduna da kuma wasu sassan Zamfara.

Kwamishinan ya bayyana cewa, sun yi nasarar ceto shi ne ta hanyar amfani da salon aiki daban-daban, inda ya ƙara da cewa rundunar za ta cigaba da aiki tuƙuru wajen daƙile ayyukan garkuwa da wasu miyagun laifuka a jihar.

A nasa ɓangaren, Gwamna Abba ya yaba wa kwamishinan ‘yan sandan da sauran jami’an da suka taimaka wajen cimma nasarar kamar su CSP Aliyu Muhammad Auwal; CSP Ado Muhammad Audi; da Kakakin rundunar CSP Abdullahi Kiyawa, sannan ya kuma umarci kwamishinan lafiyar jihar da ya tabbatar da bai wa Beli dukkan kulawar lafiyar da yake buƙata.

By Babaji

Leave a Reply