Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Alhaji Abba Dahiru Mangal, ɗan takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar Jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar APC, ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa domin shirin zaɓen 2027.
A jawabin da ya gabatar a taron magoya bayan jam’iyyar da aka gudanar a Katsina, Mangal ya ce jam’iyyar APC na buƙatar sadauƙarwa da haɗin kai daga kowane mataki domin samun nasara mai ƙarfi.
Ya ce: “Ya kamata magoya bayan jam’iyyar APC su nemi mutane don nasarar jam’iyyar daga sama har ƙasa.”
Ya ƙara da cewa: “Muna kira ga dukkan magoya bayan APC da su fito su yi aiki tuƙuru daga sama har ƙasa. Nasara ba za ta zo ba sai da haɗin kai da jajircewa.”
Jiga jigan ya’yan jam’iyyar a jihar da suka haɗa da Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa da tsohon mataimakin gwamna Tukur Ahmed Jiƙamshi da ɗan majalissar wakilai Hon Sani Aliyu Ɗanlami.
Akwai kuma shugabannin jam’iyyar APC na ƙananan hukumomi da dama da matasa da mata.
