CJN Kekere Ekun ta gargaɗi alƙalan zaɓe kan matsin siyasa yayin rantsar da su

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Alƙalin Alƙalan Nijeriya (CJN), Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta rantsar da sababbin mambobin Kwamitin Shari’o’in Zaɓe gabanin zaɓukan 2027, inda ta buƙaci da su kasance masu riƙo da gaskiya da adalci yayin hukunci ba tare da tsoro ko alfarma ba.

An gudanar da taron naɗin ne a ɗakin taro na Body of Benchers Auditorium da ke Abuja a yau Litinin 9 ga Nuwamba, 2026 wanda ya daidai da lokacin taron ƙara wa juna sani karo na biyu na Kundin Shari’o’in Zaɓe ga masana shari’a.

Da take jawabi, Mai Shari’a Kekere-Ekun ta yi kira ga alƙalan da su kasance amintattu wajen sauke nauye-nauyen da aka ɗora musu tare da daƙile dukkan wani kutsen siyasa a harkokinsu, yayin da ake shirin gudanar da wani zaɓe a Nijeriya. Saidai takardar da aka samu wannan jawabi a cikinta ba ta bayyana sunan ainihin wanda ya jagoranci fitar da ita ba.

Ta bayyana muhimmancin zaɓukan da ke tafe, inda ta ce za a yi na Shugaban Ƙasa da Majalisar Dokokin Ƙasa a ranar 16 ga Junairu, 2027, yayin da a ranar 6 ga Fabarairu kuma za a yi na Gwamnoni da Majalisun Dokokin Jihohi. Shugaban alƙalan ta tunatar da ‘yan kwamitin shari’un cewa hukunce-hukuncen dokokin ƙasa sun samar da lokacin aiki kan shari’o’in zaɓe, waɗanda ba su bada ƙofa ga wani jinkiri, tsawaita sauraron ƙararraki ko rashin kula da shari’a yadda ya dace ba.

Ta kuma gargaɗi lauyoyi, jam’iyyun siyasa da kafafen yaɗa labarai da ɗaukacin al’ummar ƙasa cewa akan aikata laifukan da suka saɓa wa doka, ciki har da bijire wa umarnin kotu da yaƙin neman zaɓe ta Soshiyal Mediya da ke isar da saƙonnin da suke warware hukunce-hukuncen kotu ko wulaƙanta jami’an shari’a.

A ƙarshe, ta ce wajibi ne wajen bai wa dimukraɗiyya kariya a samu kowane ɓangare ya sauke nauyin da ke kansa, ciki har da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), hukumomin tsaro da kuma masana shari’a, tana mai jaddada kira a gare su da su tabbatar yin hukunci kan shari’o’i bisa gaskiya da adalci a ƙarƙashin abin da ya bayyana a gare su na hujjoji.

By Babaji

Leave a Reply