
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin aka fitar da sunayen zaƙaƙuran ‘yan wasa 11 na duniya na FIFPRO, matakin da ya janyo muhawara ganin cewa babu sunan ɗan wasa Harry Kane da ya lashe kyautar Ballon d’Or ta 2026.
A cewar Sky Sports, rashin ganin Harry cikin sahun ‘yan wasan ya nuna cewa wannan shi ne karo na farko a tarihin Ballon d’Or da wanda ya lashe ya kasa shiga sahun ‘yan FIFPRO na shekarar.
Sama da ƙwararrun ‘yan wasan ƙwallon ƙafa 26,000 daga ƙasashe 75 ne suka shiga zaɓen zakarun, wanda ya samar da tsarin mai ban ƙaye. Kylian Mbappe na Real Madrid ne ya jagoranci ‘yan wasan da ƙuri’u 9,105. Sai zakaran ɗan ƙwallon ƙafar duniya, Lionel Messi, wanda ya sake shiga sahun ‘yan wasan karo 18 kuma mafi yawa a tarihi. Lamine Yamal na Barcelona ya zama ɗan wasan da aka zaɓa a FIFPRO 11 sau biyu gabanin ya kai shekara 20.
An yi zaɓin ne na bana a salon 3-4-3:
Mai tsaron gida: David Raya (Arsenal)
‘Yan baya: Pau Cubarsi (Barcelona), Achraf Hakimi (PSG), Nuno Mendes (PSG)
‘Yan tsakiya: Rodri (Manchester City), Jude Bellingham (Real Madrid), Vitinha (PSG)
‘Yan gaba: Erling Haaland (Manchester City), Kylian Mbappe (Real Madrid), Lionel Messi (Inter Miami), Lamine Yamal (Barcelona)

Sai ɓangare mata, inda ‘yar wasan tsakiya ta Barcelona, Aitana Bonmati ta lashe zaɓen, inda samu ƙuri’a 3,083. ‘Yar wasan baya ta Chelsea, Lucy Bronze ta sake shiga sahun ‘yan wasan karo na 11 a tarihinta, wanda ya sa ta zama ‘yar wasa mafi samun gurbi a sahun ƙwararrun.

