Sokoto: Yadda Atiku da DSS sun yi musayar yawu kan zargin tarwatsa gangamin ADC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya zargi Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da ɗaukar nauyin wasu masu zanga-zanga domin tarwatsa gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyarsa a Jihar Sakkwato.

Sai dai hukumar ta musanta zargin, duk da cewa ta bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin. Atiku ya bayyana zargin ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ranar Talata. Ya ce shirin gudanar da zanga-zangar wani yunkuri ne na haddasa hargitsi, domin ba wa gwamnatin jihar damar kafa dokar hana fita tare da hana ADC gudanar da gangaminta a ranar da aka tsara.

Ya kuma zargi gwamnatin Jihar Sakkwato da kawo cikas ga shirye-shiryen jam’iyyar, ta hanyar hana ta amfani da wasu wuraren taron jama’a da kuma ƙin bayar da tallafin kayan aiki da ake buƙata domin gudanar da harkokin yaƙin neman zaɓenta.

Atiku ya bayyana cewa waɗannan matakai da ake zargin an ɗauka, ƙoƙari ne na ganganci na hana ADC samun damar yin fafatawa da sauran jam’iyyu cikin ’yanci da daidaito gabanin babban zaɓen 2027. Ya ce, “Abin da ya fi tayar da hankali shi ne bayanan da muka samu na cewa shugabannin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya na ɗaukar mutane domin su shirya zanga-zanga a Sakkwato.”

Atiku ya yi zargin cewa an tattara wasu daga cikin masu zanga-zangar ne a wani ofishi da ke bayan bankin Zenith, a kan titin Koko, inda ake zargin an tura manyan motoci zuwa wasu muhimman wurare, ciki har da wata mahaɗar hanya mai zagaye.

Ya kuma yi iƙirarin cewa masu zanga-zangar na haddasa cunkoson ababen hawa, barazana ga matafiya da kuma dukan wasu mazauna yankin. “Wannan ba aikin leƙen asiri ba ne. Tsoma baki ne a harkokin siyasa da aka ɓoye a cikin kayan aikin hukuma,” inji tsohon mataimakin shugaban ƙasar.

Ya buƙaci jami’an tsaro da ake zargin suna da hannu a shirin da su janye daga wannan mataki, yana mai cewa ya kamata hukumomin tsaro su kare ’yan Nijeriya da tabbatar da bin doka, maimakon shiga harkokin siyasa da nuna goyon baya ga wata jam’iyya. Atiku ya kuma zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da raunana jam’iyyun adawa tare da rage damar fafatawar siyasa, ta hanyar abin da ya kira siyasar haɗiye ’yan adawa da kuma tsoratar da su.

Ya yi zargin cewa gwamnati na ƙoƙarin mayar da Nijeriya ƙasa mai jam’iyya guda, ta hanyar jan hankalin manyan ’yan adawa su koma jam’iyyar APC mai mulki. ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC ya ce maimakon gwamnati ta riƙa kawo cikas ga gangamin jam’iyyun adawa, ya kamata ta mayar da hankali wajen magance tsadar rayuwa da ke ƙara addabar al’umma.

Ya lissafa tsadar kayan abinci, sufuri, man fetur da wutar lantarki a matsayin wasu daga cikin manyan matsalolin da ’yan Nijeriya ke fuskanta, yana mai cewa iyalai da dama na shan wahala wajen samun abubuwan yau da kullum. Atiku ya yi alƙawarin cewa idan ADC ta kafa gwamnati, za ta ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida, bunƙasa noman abinci, samar da ayyukan yi da kuma rage kuɗin gudanar da harkokin kasuwanci. Ya kuma gabatar da shawarar bayar da tallafin samar da kayayyaki da aka tsara bisa buƙata, wanda za a danganta da man fetur da aka tace a Nijeriya.

A cewarsa, wannan tsari zai rage wa masu amfani da mai nauyin kuɗi, tare da ƙarfafa masana’antun cikin gida. Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya zargi jam’iyyar APC da komawa ga dabarun tsoratarwa, sakamakon abin da ya bayyana a matsayin rashin nasarar da jam’iyyar ta samu a gangaminta na baya-bayan nan a Kaduna. Duk da haka, ya jaddada cewa ƙoƙarin da ake zargin ana yi na kawo cikas ga ADC ba zai hana jam’iyyar ci gaba da yaƙin neman zaɓenta ba.

Sai dai a cikin wata sanarwa da ta fitar a daren Laraba, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta musanta zargin cewa tana ɗaukar nauyin masu zanga-zanga domin tarwatsa gangamin ADC a Jihar Sakkwato. Sanarwar, wadda Favour Dozie, Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a da Sadarwa ta Dabaru na hukumar ya sanya wa hannu, ta ce an jawo hankalin Babban Daraktan DSS kan zargin da Atiku ya yi na cewa hukumar na shirya zanga-zanga a jihar.

Hukumar ta ce, “Domin fayyace gaskiyar lamarin, jami’an DSS da aka tura domin kare ɗan takarar gwamnan ADC na Sakkwato, Mannir Daniya, sun kwashe shi zuwa wurin tsira cikin ƙoshin lafiya a ranar 31 ga Oktoban 2026, bayan an kai masa hari a Sakkwato. An kuma kai wa jami’an DSS biyu hari a yayin wannan lamarin, kuma har yanzu suna karɓar magani a asibiti. ɗan takarar gwamnan ya kira Daraktan Hukumar na Jihar Sakkwato da kansa domin nuna godiya, har ma ya nemi ƙarin jami’an tsaro daga hukumar.”

DSS ta kuma tuna cewa a ranar 2 ga Maris, 2026, ta kama Monday Udeme Steven a Jihar Ribas, bisa zargin yin barazanar kai hari ga Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC. A cewar hukumar, ta gurfanar da Steven a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Ribas, inda aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari.

Hukumar ta ce ayyukan da ta gudanar domin kare ’yan jam’iyyun siyasa sun saɓa wa zargin da Atiku ya yi, kuma irin waɗannan zarge-zarge na iya karya gwiwar jami’anta waɗanda ke sadaukar da rayukansu wajen gudanar da aikinsu. Sanarwar ta wara da cewa, “Duk da cewa waɗannan ayyukan da muke yi domin kare dukkan jam’iyyun siyasa sun saɓa wa zargin da wannan dattijon ɗan siyasa ya yi, kuma hakan na iya karya gwiwar jajirtattun jami’anmu da ke jefa rayukansu cikin haɗari yayin gudanar da aiki, Babban Daraktan DSS ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan zargin, saboda girmama wannan dattijon ɗan siyasa.”

DSS ta kuma yi nuni da wani makamancin zargi da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, ya yi, inda ya zargi hukumar da hannu a harin da aka kai masa a Jihar Ekiti.

Dangane da wannan batu, hukumar ta yaba wa Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya bisa abin da ta kira bincike cikin gaggawa da kuma rahoton farko da ta fitar, wanda ya danganta lamarin da wani saɓani tsakanin mutane. Rundunar ’yan sandan ta kuma kama waɗanda ake zargi su 11. DSS ta ce tana jiran sakamakon cikakken binciken ’yan sanda, kuma ba za ta ɓata lokacinta da ƙarfinta wajen ci gaba da magana kan lamarin ba.

By ukarofi

Leave a Reply