Ɓarkewar kwalara ta yi ajalin fursunoni a kurkukun Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu fursunoni guda biyu sun rasu bayan ɓarkewar cutar kwalara a gidan gyaran hali na Kurmawa da ke Jihar Kano.

Hukumar kula da Gidajen Gyaran Hali ta Ƙasa (NCoS) ce ta tabbatar da ɓarkewar cutar a wata takarda da ta fitar a ranar Asabar, inda ta ce tuni aka ɗauki matakin kula da halin kuma a yanzu babu wani rahoton mutuwa bayan na mutane biyu.

A cewar sanarwar da Kakakin hukumar, CSC JN Osuji ya fitar, wani binciken lafiya da aka gudanar a ranar 23 ga Satumba ne ya tabbatar da ɓarkewar cutar. Ya ce, a ranar 17 ga Satumba ne aka fara ganin alamarta a jikin wani fursuna ciki har da amai da gudawa.

Akan haka ne aka gaggauta kai shi asibitin cibiyar, yayin da aka ɗauki matakan lafiya an gaggawa a washe-gari domin tabbatar da guje wa yaɗuwarta acikin fursunoni.

Ya kuma ce, Kwantirola Janar na NCoS, Sylvester Nwakuche ya umarci a gaggauta ɗaukar matakan lafiya da suka dace da kariya ga cutar tare da haɗin-gwiwar Gwamnatin Kano.

Ya ƙara da cewa, an tura wata tawaga ta musamman daga hedikwatar hukumar ta ƙasa domin sanya ido kan matakan da aka ɗaukar yayin da ake ƙoƙarin shawo kan al’amarin.

By Babaji

Leave a Reply