
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026 Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da bayar da kyautar Naira miliyan 100 ga kowace ɗaya daga cikin ‘yan wasan tawagar Flamingos bisa nasarar lashe Kofin Duniya na mata da hukumar FIFA ta shirya na ‘yan ƙasa da shekara 17.
Tawagar Nijeriyar ta doke Japan ne da 2 da 1 a wasan ƙarshe, nasarar da ya ba ta damar lashe kofin wanda aka gudanar da wasanninsa a Moroko.
Da take jawabi a lokacin da tawagar da jami’an horarwa suka ziyarci Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta sanar da bayar da ladar, inda ta ce ƙasar na alfahari da su. Ta bayyana cewa, za a ajiye kuɗaɗen ga matasan ‘yan wasan a wasu bankuna da aka amince da su.
Haka ma kociyan ‘yan wasan an ba shi Naira miliyan 100, yayin da sauran ‘yan tawagar gudanarwarsu suka samu miliyan N50 kowanne. “Ina nan ne yau don wakiltar Shugaban ƙasa, saboda kuna tsammanin ganin Shugaban a yau. Kun san idan aka ce, ‘in kuka gan ni, kun ga Uban.’ Idan kuka gan ni kun ga Shugaba,” inji ta.
Oluremi ta bayyana cewa, an ɗauki matakin ajiye musu kuɗaɗen nasu a wasu bankuna ne da nufin adana musu duba da cewa sun kasance ‘yan ƙasa da shekara 17, tana mai miƙa godiyarsu a gare su kan zuwa fadar da kiran su cigaba da zama masu addu’o’i don cigaba da cimma nasarori a nan gaba.
