Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Madugun adawa a Katsina Dr. Mustapha Muhammad Inuwa da dubban magoya bayansa sun fice daga ADC sun koma APC.
Mustapha Inuwa wanda tsohon sakataren gwamnatin Jihar Katsina dama can ɗan jam’iyar APC amma tun da jam’iyar ta gudanar da zaɓen fidda ɗan takara gwamna, da Dikko Raɗɗa ya kada shi ya bar jam’iyar.
Bayan wani lokaci sai madugun adawar ya koma jam’iyar PDP nan ma ya fice bayan ya sami saɓani da Sanata Yakubu Lado Danmarke.
Daga nan ya koma ADC inda ya zama jagorar jam’iyar a Jihar kafin shigar shi APC.
Sauyin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, yayin da ake kallon matakin a matsayin wani gagarumin ci gaba ga APC a jihar.
Da yake jawabi bayan sanar da ficewa daga jam’iyar ADC, Dr Mustafa Inuwa ya ce ” Shiga jam’iyar APC ita ce mafita a gare mu”ya ce daga yau kowa ya je ya rubuta takardar barin jam’iyar ADC.
Ya bayyana cewa Gwamna Dikko Raɗɗa ya yi masa alƙawarin ɗaukar shawarwarin sa don ciyar da Jihar gaba,yayi fatan Allah sa shigar su cikin Jam’iyar APC ya zama alheri ga al’ummar Jihar Katsina.
Mustapha Inuwa ya fice daga jam’iyar ADC ne sakamakon rashin jetuwa da ya sami da jiga jigan ya’yan jam’iyar kan abinda ya kira rashin adalici wajan fidda ɗan takarar kujerar gwamnan Jihar wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka yi takara.
A yanzu da Sanata Ahamed Babba Kaita jam’iyar ADC ta fidda zai mata takarar kujerar gwamnan Jihar.
Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa shigowar Dr. Mustapha Muhammad Inuwa da mabiyansa APC zai iya ƙara wa jam’iyyar ƙarfi a shirye-shiryenta na zaɓuka masu zuwa.
