An kama wani mai aski mai suna Emeka a garin Umuahia, babban birnin Jihar Abia, bayan da jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Abia suka gano wata tukunya da ke cike da gashin mutane a cikin ɗakinsa.
Rahotanni sun ce Emeka ya yi suna a Umuahia saboda ƙwarewarsa wajen aski, sai dai an cafke shi ne a ranar Talata bayan maƙwabcinsa, Johnson Ikenga, ya kai ƙorafi ga ‘yan sanda yana zargin mai askin da yi masa barazana.
A yayin da jami’an ‘yan sanda suka kai samame gidan wanda ake zargin domin bincike, sun gano wata tukunya mai ɗauke da gashin mutane tare da wasu kayayyakin da ake alaƙanta da ayyukan tsafi.
Bayan kama shi, Emeka ya amsa cewa tukunyar tasa ce, amma ya gaza bayyana abin da yake amfani da gashin da sauran kayayyakin wajen yi. Haka kuma, bai yi bayani kan yadda ya samo gashin ba.
Sai dai mazauna yankin da dama na zargin cewa gashin da aka samu na iya kasancewa na kwastomomin da suka saba zuwa shagonsa domin yin aski.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Abia ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba. Sai dai an kai wanda ake zargin zuwa Ofishin ‘Yan Sanda na Tsakiya, Umuahia, domin ci gaba da bincike.
