Wasu yara biyu sun jikkata bayan da mahaifinsu ya jefa su daga saman wani bene mai hawa uku a unguwar Umuobe da ke kusa da Babban Garin Aba, a Jihar Abia.
Rahotanni sun ce mutumin, mai kimanin shekara 40 a duniya, ya aikata hakan ne saboda wani dalili da har yanzu ba a bayyana ba.
Bayan jefa yaran, shi ma ya yi tsalle daga saman wannan bene, bayan da ake zargin ya yi barazanar cutar da matarsa.
Ko da yake yaran sun tsallake rijiya da baya, sun samu raunuka daban-daban sakamakon faɗuwar.
Mazauna yankin, da suka fito bayan jin kukan yaran, sun garzaya wajen da lamarin ya faru, inda suka ceto su tare da kai su asibiti domin samun kulawar likitoci.
Daga nan ne aka sanar da Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, wadda ta tura jami’anta zuwa wurin cikin gaggawa.
Da isarsu, jami’an sun cafke mahaifin yaran, sannan aka kai shi wani asibiti daban da wanda ake kula da yaran da suka jikkata.
Wasu mazauna yankin sun yi hasashen cewa wataƙila shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ne suka janyo mutumin aikata wannan mummunan abu, yayin da wasu kuma ke zargin wata matsala ta rashin lafiyar ƙwaƙwalwa.
Da take tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Abia, DSP Maureen Chinaka, ta ce an fara gudanar da bincike domin gano musabbabin abin da ya faru.
Ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Alhamis, 30 ga Yuli, 2026.
A cewarta, “Mun samu rahoton cewa wani matashi ya jefa ‘ya’yansa biyu daga hawa na uku na wani bene, sannan shi ma ya yi tsalle daga wannan tsayin.
“Mun isa wurin cikin gaggawa. Yaran suna samun kulawa a wani asibiti, yayin da mahaifinsu ke kwance a wani asibiti daban. Bincike na ci gaba.”
